Aminiya:
2025-09-20@09:21:26 GMT

Ɗan ƙunar baƙin wake ya kashe mutum 10 da bam a Borno

Published: 21st, June 2025 GMT

Aƙalla mutum 10 ne suka rasu a daren ranar Juma’a bayan wani ɗan ƙunar baƙin wake ya kai hari da bam a wani wsjen cin abinci da ke garin Konduga, a Jihar Borno.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Borno, ASP Nahum Daso, ya tabbatar da faruwar lamarin.

’Yan Najeriya da suka maƙale a Isra’ila na neman ɗauki Bam ya kashe mutum 5, 15 sun jikkata a Kano

Ya ce jami’an tsaro da suka haɗa da ‘yan sanda da sojoji na gudanar da bincike domin gano haƙiƙanin abin da ya faru da kuma adadin waɗanda lamarin ya rutsa da su.

Ya ce, “Wani mutum ya kutsa cikin taron mutane da misalin ƙarfe 10 na dare tare da bam, wanda ya tarwatsa kansa kuma ya kashe sama da mutum 10.”

Wani masani kan ta’addanci, Zagazola Makama, ya bayyana cewa mutum 24 ne, suka rasu a sanadin harin, inda ya ce mace ce ta kai harin ƙunar baƙin waken.

Ya ƙara da cewa fashewar ta yi tsanani wanda sai kan matar aka samu.

Bayan harin, an tura tawagar sojoji, ƙwararrun masu binciken bam na ‘yan sanda, ’yan sa-kai, da ƙungiyar CJTF zuwa wajen.

Sun yi bincike amma ba su samu bam na biyu a wajen ba.

An kwashe waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH) domin a kula da su.

An kai gawarwakin waɗanda suka rasu zuwa asibitin kuma likitoci sun tabbatar da rasuwarsu.

Makama, ya ce ana ci gaba da tantance sunayen waɗanda abin ya rutsa da su domin a miƙa gawarwakinsu ga iyalansu domin yi musu jana’iza.

Kai harin ƙunar baƙin wake na ɗaya daga cikin dabarun da ƙungiyar Boko Haram ta fara amfani da su a farko-farkon fara ta’addancinta a Najeriya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda Ɗan Ƙunar Baƙin Wake hari Wajen Cin Abinci ƙunar baƙin

এছাড়াও পড়ুন:

Fubara ya sauka a filin jirgin saman Fatakwal

Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya dawo bayan shafe tsawon lokaci baya jihar biyo bayan sanya dokar ta-ɓaci da  Shugaba Tinubu ya yi.

A ranar Laraba ne Shugaba Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci, wadda tsohon Hafsan sojan ruwa, Vice Admiral Ibok-Ekwe Ibas (rtd), ya jagoranta.

’Yan bindiga sun kai hari sakatariyar ’yan jarida ta jihar Yobe An dakatar da shugabannin sakandare 6 a Sakkwato kan zargin cin amanar aiki

Magoya bayan gwamnan sun taru a gidan gwamnatin jihar da ke Fatakwal domin tarbarsa bayan dakatar da shi na tsawon watanni shida, amma daga baya suka watse bayan shafe lokaci suna jira ba tare da ganinsa ba.

Da safiyar ranar Juma’a, magoya bayan suka koma Filin Jirgin Sama na Fatakwal.

Jirgin da ya ɗauko gwamnan ya sauka a filin da misalin ƙarfe 12 na rana.

Ya gaisa da magoya bayansa a filin jirgin kafin daga bisani ya shiga mota tare da ayarinsa suka tafi.

Babu tabbacin cewar ko gidan gwamnati ya nufa kai-tsaye domin ci gaba da gudanar da harkokin mulki.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Takari: Rayuwar baƙin haure ’yan Najeriya mazauna Saudiyya
  • Fubara ya sauka a filin jirgin saman Fatakwal
  • Mutum 1,666 ne suka kashe kansu a Legas cikin shekaru biyar – ’Yan sanda
  • Cutar Kwalara ta kashe mutum 58 a Bauchi
  • Yadda jariri ya rasu a bayan mahaifiyarsa yayin tsere wa harin ’yan bindiga a Neja
  • An kashe ’yan ta’addan IPOB da yawa a Imo — ’Yan Sanda
  • ’Yansanda Sun Kama Mutane 9 Kan Yin Ƙaryar Sace Su A Jihar Neja
  • Gobara ta kashe manyan jami’an hukumar FIRS 4 a Legas
  • Sojoji Sun Kashe Mayaƙan ISWAP 11 A Borno Da Adamawa
  • ‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja