Koriya ta Arewa za ta taimaka wa Iran gyara tashoshin nukiliyan da Amurka ta kai hari —Masani
Published: 23rd, June 2025 GMT
Akwai yiwuwar ƙasar Koriya ta Arewa mai ƙarfin makaman nukiliya za ta taimaka wajen gyara tashoshin nukiliyan Iran da hare-haren Amurka suka lalata da kuma gina sababbin masana’antun ƙera makamai masu linzami masu gudun walƙilya a Iran.
Wani masani mai suna Ankit Panda daga cibiyar zaman lafiya ta kasa da kasa ta da ke Amurka, ne ya bayyana hakan, baya Amurka ta kai hare-hare kan tashoshin nukiliya na ƙasar Iran.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito Ankit Panda, yana bayyana cewa matakin zai kawo ƙarshen irin takura da ƙasashen Yamma ke yi wa Iran.
Hakan na zuwa ne bayan da Ma’aikatar Harkokin Wajen Koriya ta Arewa ta yi tir da harin da Amurka ta kai a matsayin keta hurumin ’yanci da kuma tsaron ƙasar Iran.
NAJERIYA A YAU: Matakan daƙile kisan matafiya a hanyoyin Najeriya Mutum 2 sun mutu a ƙoƙarin ciro waya daga masai a KanoHakan na zuwa ne bayan da Ma’aikatar Harkokin Wajen Koriya ta Arewa ta yi tir da harin da Amurka ta kai a matsayin keta hurumin ’yanci da kuma tsaron ƙasar Iran.
Ta bayyana cewa, “Amurka da Isra’ila su ne kanwa uwar gani a rikici a yankin Gabas ta Tsakiya, sakamakon yake-yake da ƙoƙarin Isra’ila na faɗaɗa girman ƙasarta, tare sa smaun goyon bayan ƙasashen Yamma.
“Ya kamata al’ummomin duniya masu goyon bayan adalci su fito da murya ɗaya aula’anci wannan abin da Amurka da Isra’ila ke yi, kuma su taka musu burki,” in ji sanarwar da kamfanin dillancin labarai na Koriya ta Arewa (KCNA) ya ruwaito.
Ƙawancen soji tsakanin Iran da Koriya ta Arewa ta jima, kuma ana zargin ta taimaka musu wajen haɗawa da musayar makamai masu linzami masu gudun walƙilya masu cin dogon zango.
Ankit ya ce ba lallai ne Koriya ta Arewa ta taimaka wa Iran wurin ginawa ko hanzarta ƙera makaman nukiliya ba, domin gudun kada makaman su je Amurka. Idan hakan ya faru, Amurka na iya gano lagon fasahar makaman Koriya ta Arewar.
Amma dai akwai yiwuwar Koriya ta Arewar za ta iya, lura da yadda ke da ƙwarewa wajen fasahar makamai da kuma yadda a baya da yawaita taimako ta wannan bangare ga Rasha, wata babbar ƙawar Iran.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Iran Isra ila Koriya ta Arewa nukiliya Koriya ta Arewa ta
এছাড়াও পড়ুন:
Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Sun Jaddada Shirinsu Na Tunkarar Duk Wata Barazana
Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun jaddada cewa: Duk wata barazana ga tsaron Iran za ta fuskanci kakkausan martani mai zafi fiye da tunani
Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun fitar da sanarwar cikan kwanaki 40 da shahadar shahidan Iran a lokacin wuce gona da iri na yahudawan sahayoniyya da Amurka, inda suka jaddada cewa: Duk wata barazana ga tsaro da yankin kasar Iran za ta fuskanci kakkausar martani da ya zarce tunanin makiya, kuma zasu kasance mafi tsanani fiye da abin da ya faru gamakiya da amsu kiran yaki a martanin alkawarin gaskiya na uku.
A cikin wata sanarwa da Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran suka fitar a cikan kwanaki arba’in da shahadar gwarazan kasa Dakarun IRGC sun jaddada cewa: Suna tare da sauran jami’an kasar a kodayaushe kuma suna shirye wajen mayar da martani mai tsauri da kakkausan mayar da martini kan duk wata barazana ko ta’addanci daga Amurka ko ‘yan sahayoniyya ko kuma kawayensu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hare-Haren Sojojin Mamayar Isra’ila Kan Gaza Sun Janyo Shahadan Falasdinawa Masu Yawa August 7, 2025 Human Rights Watch Ta Ce: Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Rusa Makarantu Fiye Da 500 A Gaza August 7, 2025 Amurka Ta Kwace Dalar Amurka Miliyon $584 Na Jami’ar California Saboda Gaza August 7, 2025 Mutanen Kasar Lebanon Suna Tsoron HKI Zata Shiga Kasar Daga Kasar Siriya August 7, 2025 Amurka ta Fara Janye Wasu Sojojinta Daga Wurare 3 A Kasashen Iraki Da Siriya August 7, 2025 Kasar Masar Ta Zama Mai Shiga Tsakanin Iran Da IAEA Da Kuma Amurka August 7, 2025 Araqchi: Ba a kayyade wani lokacin shiga wata sabuwar tattaunawa da Amurka ba August 7, 2025 Ghana: Ministocin tsaro da muhalli sun rasa rayukansu a hatsarin jirgi mai saukar ungulu August 7, 2025 Jamus: Shahararrun mutane da ‘yan jarida sun bukaci a daina baiwa Israila makamai August 7, 2025 Gaza: Fararen hula 22 sun yi shahada a hare-haren Isra’ila a daren jiya August 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci