Nijeriya Da Brazil Sun Ƙulla Yarjejeniyar Horar Da Matasa Kiwon Dabbobi
Published: 23rd, June 2025 GMT
Idi ya kuma yi nazari kan matakin da bangaren kiwon dabbobin kasar yake, inda yawan Shanu suka kai miliyan 20.9, Tumaki miliyan 49.1, Awakai miliyan 88.2, Kajin gidan gona kuma miliyan 258.5.
Kazalika, Maiha ya jaddada muhimmancin hadakar ta zuba hannun jari a fannin na kiwon dabbobin, wanda ya sanar da cewa; hakan zai taimaka matuka gaya wajen dakile yaduwar cututtukan da ke yi wa dabbobin illa.
A nasa jawabin, Babban Shugaban Kamfanin Ricardo Lacerda ya bayyana cewa; kasar Brazil na shirin samar da wuraren kiwon dabbobi na zamani kimanin guda 200,000 a wasu daga cikin jihohin wannan kasa, musamman don kara samar da isasshen naman Shanu.
Ya kara da cewa, kasar za kuma ta tabbatar da kokarin kara habaka bangaren kiwon Kajin gidan gona, duk dai a cikin wannan shiri.
Har ila yau, kamfanin ya sake zabo Jihar Ogun, domin tabbatar da ganin ta amfana da shirin, kazalika; kamfanin na yukurin zuba hannun jari na kimanin dala biliyan 2.5, duba da cewa; jihar ita ce ta kasance kan gaba wajen aiwatar da kiwon Kajin gidan gona a dukkanin fadin Nijeriya.
Wani mai zuba hannun jari a kamfanin Wesley Batista ne ya tabbatar da hakan, lokacin da wasu jami’an kamfaninsa, suka kai ziyara; wanda John Coumantaros ya jagoranta zuwa wurin Gwamnan Jihar Ogun Dapo Abiodun, a fadar gwamnatin jihar, da ke garin Abeokuta.
Batista ya sanar da cewa, Allah ya albarkaci kasar nan da albarkatun kasa da dama, wanda ya sanar da cewa; za su yi amfani da ilimin da suke da shi da kuma kwarewarsu a wannan bangare na kiwon dabbobi, musamman domin samun damar kara habaka tattalin arzikin kasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Batun Ceto Wanda Ake Zargi Da Kwaya: Kwamishinan Kano Ya Yi Murabus
Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Ali Namadi, ya ajiye aikinsa bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoton kwamitin bincike da ke duba rawar da ya taka a batun ceto wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu.
Wannan matakin na murabus ana kallonsa a matsayin wani muhimmin cigaba da ke nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen kare gaskiya, bayyana ta da kuma ɗaukar nauyin ayyukanta a bainar jama’a.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, Kwamishinan ya bayyana cewa ya yanke shawarar murabus ne duba da muhimmancin al’amuran da suka shafi jama’a da kuma halin da ake ciki.
Ya ce: “A matsayina na ɗaya daga cikin masu fada-a-ji a wannan gwamnati da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, ya dace na ɗauki wannan mataki, koda kuwa zai sosa zukata.
“Ko da yake ina ci gaba da musanta hannuna a lamarin, ba zan iya watsi da irin yadda jama’a ke kallon batun ba, da kuma bukatar kare ƙimar gwamnati da muka ginata tare.” In ji shi.
Alhaji Namadi ya nuna godiya ta musamman ga Gwamna Abba Kabir Yusuf saboda ba shi damar yi wa jiharsa hidima, tare da jaddada aniyarsa ta ci gaba da bin manufofin gwamnatin.
Ya ƙara da cewa: “A matsayina na ɗan ƙasa nagari, dole ne in ci gaba da kare amana da hangen nesan da muka haɗa kai wajen shimfiɗawa a jiharmu. Zan ci gaba da kasancewa mai biyayya ga akidun da suka kawo wannan gwamnati kan mulki.”
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi murabus ɗin cikin farin ciki, tare da yi masa fatan alheri a duk wani yunƙurinsa na gaba.
Gwamnan ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa wajen tabbatar da adalci, ladabi, da kuma yaki da miyagun dabi’u da laifukan da suka shafi kwayoyi da sauran matsalolin da ke shafan matasa da al’umma baki ɗaya.
Ya kuma ja hankalin duk masu rike da mukaman siyasa da su kasance masu hikima da taka-tsantsan wajen hulɗa da al’amuran jama’a, tare da neman izini daga hukumomi mafi girma kafin su shiga cikin wani lamari da ke da tasiri a bainar jama’a.
Abdullahi Jalaluddeen