Mahaifiyar Babban Editan jaridar Daily Trust ta rasu
Published: 23rd, June 2025 GMT
Allah Ya yi wa mahaifiyar Babban Editan Jaridar Daily Trust, Hamza Idris rasuwa.
Kaninsa, mai suna Aminu Idris, ya bayyana cewa a safiyar Litinin ne Allah Ya yi wa mahaifiyar Babban Editan, Hajiya Rabi (Umma) cikawa bayan gajeruwar jinya a Jihar Kano.
Za a gudanar da jana’izarta kamar yadda addinin Musulunci ya ranar a Layin Ɗorawar ’Yan Kifi da ke unguwar, Rijiyar Zaki, Kano.
Daga nan za a kai ya maƙabartar Walid Mai Zage da ke Kofar Mazugal.
Muna roƙon Allah Ya yi mata rahama, Ya ba wa dangi haƙurin rashin da kuma dangana.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Babban Editan Jaridar Daily Trust mahaifiyar
এছাড়াও পড়ুন:
Kwamishina ya yi murabus kan ƙarbar belin dillalin ƙwayoyi a Kano
Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Ali Namadi, ya yi murabus daga muƙaminsa saboda ce-ce-ku-ce da ya biyo bayan karɓar belin wani wanda ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi da ya yi.
Namadi ya yi murabus ne sa’o’i kaɗan bayan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoton kwamitin bincike da ya kafa kan lamarin.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Namadi ya ce ya yanke shawarar yin murabus ne don “amfanin jama’a gaba daya” da kuma kare gwamnatin a “yaƙin da take yi da sayarwa da shan miyagun kwayoyi.”
Sai dai ya dage kan cewa ba shi da laifi, amma ya yarda cewa ra’ayin jama’a na da muhimmanci, kuma yana da kyau ya kare kimar gwamnatin.
Tuni Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi murabus ɗin tare da yi wa tsohon kwamishinan fatan alheri.
Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya ce Gwamnatin Jihar Kano na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da adalci da yaƙi da laifukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi.
Gwamna Abba ya kuma jaddada muhimmancin dukkan jami’an gwamnati su riƙa yin taka-tsantsan da neman izini daga manyan hukumomi kan batutuwa masu mahimmanci na jama’a.