Kotu ta saki tsohon shugaban Koriya ta Kudu, Yoon Suk Yeol
Published: 8th, March 2025 GMT
Wata kotu a Koriya ta Kudu, ta saki tsohon shugaban ƙasar, Yoon Suk Yeol, bayan da ta yi watsi da kama shi, duk da cewa ana ci gaba da bincike kan zargin da ake masa.
Yoon, wanda aka dakatar daga mulki, an tsare shi ne tun a watan Janairu bayan da ake zarginsa da ƙoƙarin kifar da mulkin farar hula.
Ramadan: Hisbah ta rufe shagon caca a Kano An kashe shugaban Lakurawa, Maigemu a KebbiA ranar 3 ga watan Disamban 2024, jami’an tsaro sun kai masa samame bisa zargin tayar da zaune tsaye.
Bayan an sake shi, Yoon ya fito daga gidan yari yana murmushi, sannan ya sunkuyar da kai domin nuna godiya ga magoya bayansa da suka zo ganinsa.
A ranar Juma’a, kotu ta soke umarnin da aka bayar na kama shi, inda ta ce babu isassun hujjoji da ke tabbatar da laifin da ake zarginsa da shi.
Duk da haka, ana ci gaba da shari’a kan batun tsige shi daga mulki.
Masu gabatar da ƙara sun ce za su mayar da hankali kan gabatar da hujjoji a gaban kotu maimakon ɗaukaka ƙara kan sakinsa.
Idan har kotun tsarin mulki ta tabbatar da tsige shi, Koriya ta Kudu dole ne ta gudanar da sabon zaɓen shugaban ƙasa cikin kwanaki 60.
Duk da haka, ana sa ran za a ci gaba da shari’ar Yoon, ko da kuwa an sauke shi daga mulki gaba ɗaya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Koriya ta Kudu zargi
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun yi juyin mulki a Jamhuriyar Benin
Sojoji a kasar Jamhuriyar Benin sun kifar da gwamnati a wani juyin mulki da suka sanar a ranar Lahadi.
Sojojin sun bayyana ne a gidan talabijin na kasar inda suka sanar da tsige Shugaban Kasa Patrice Talon da kuma rushe duk hukumomin kasar.
Dakarun, karkashin jagorancin Laftanar Kanar Pascal Tigiri, sun rufe iyakokin kasar da rushe jam’iyyun siyasa.
Zuwa lokacin kammala wannan labarin babu labarin halin da Shugaba Talon wanda ke kan karagar mulkin tun a 2016 yake ciki.
Amma ministan harkokin kasar, Olusegun Ajadi Bakari, ya ce an samu yunkurin kifar da gwamnati, amma ana neman shawo kan lamarin.