Hikimar Yunƙurin Sake Farfaɗo Da Noman Filanten A Jihar Nasarawa
Published: 22nd, June 2025 GMT
Gonar ta ‘AA Dibine Agro’, ta kasance a yankin Pasali Karshi da ke cikin karamar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa.
Kazalika, kudirin shi ne; nomawa da kuma samar da isasshen Filanten din da za a rika kai wa har zuwa babban birnin tarayya Abuja, domin sayar da shi.
A cewar tasa, abin da gonar ke son cimma shi ne, taimaka wa fannin aikin noma na tarayyar kasar nan, wanda hakan zai kuma kara tallafawa wajen kara samar da ayyukan yi ga ‘yan kasa tare da samar da wadataccen abinci.
Sai dai, ya bayyana cewa; rashin kudaden da za a yi amfani da su wajen cimma wannan manufa, su ne babban cikas.
Gonar, wadda aka samar da ita a zagayen Katangu, domin kiwon dabbobi, na matukar fama da karancin ruwa da ya yi sanadiyyar dakatar da gudanar da dukkanin wasu ayyuka da ake yi a cikinta.
Bugu da kari, rashin samar da hanya; wadda za a rika amfani da ita wajen safarar amfanin gonar da aka girbe, na daya daga cikin kalubalen da gonar ke fuskanta.
Amma duk da irin wadannan matsaloli da gonar ta ‘AA Dibine’ ke fuskanta, ta tanadi wasu muhimman manya-manyan shirye-shiye.
Daga cikin shirye-shiyen sun hada da; burin samar da wuraren kiwon dabbobi da kiwon Kajin gidan gona da wuraren kiwon Kifi da kuma sarrafa abincin dabbobi, wanda hakan zai taimaka wajen habaka tattalin arzikin yankin tare da samar da ayyukan yi da kuma kara bunkasa noma.
kungiyar ta COMAFAS, ta fi mayar da hankali ne wajen tallafa wa manoma da kuma kara habaka fannin aikin noma.
A cewar Dakta Maduka, kungiyar ta amince da yarjejeniyar ce, duba da cewa; ta lura da manufar da gonar ta ‘AA Dibine Farm Limited’, ta sanya a gaba, musamman domin tsamo gonar daga cikin babban kalubalen da take fuskanta tare kuma da samun damar cimma burin da ta sanya a gaba.
Ya kara da cewa, hadakar za kuma ta taimaka wajen samar da ilimi da masu zuba hannun jari da kuma samun tallafin kudi ga gonar. Haka zalika, kudin zai taimaka, wajen sama wa gonar kayan aikin da take bukata da kuma samar da hanyar yin jigilar amfanin gonar da aka shuka.
Sauran daukin da hadakar za ta samar, sun hada da horo da kuma tabbatar da shugabanci nagari da sauran makamantansu.
Dakta Maduka, ya kuma bayar ta tabbacin cewa; ta hanyar jawo sauran abokan hadaka cikin wannan aiki, za a iya noman wannan Filanten mai matukar tarin yawa a gonar, duba da cewa; yankin na da yanayi mai kyau na yin noma da ake bukata, inda kuma hakan zai kara taimakawa wajen samar da ayyukan yi.
Kazalika, ya bayyana cewa; hadakar za kuma ta kara taimakawa wajen kara habaka tattalin arzikin yankin tare da samar da wadataccen abinci yadda ya kamata.
A cewar tasa, gonar ta ‘AA Dibine Farm Limited’, za ta kasance mai aiki da kayan noma na zamani a tsakanin sauran gonakin da ke fadin kasar nan, ta hanyar taimakon kungiyar ta COMAFAS.
Har ila yau, daukacin masu kulla wannan yarjejeniya, sun amince da kara habaka wannan bangare na noma a dukkanin fadin Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Ayaba
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnan Kano ya gargaɗi muƙarrabansa bayan murabus ɗin Kwamishina
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gargaɗi maƙarrabansa cewa duk wanda ba zai iya sauke nauyin da aka ɗora masa, ya yi murabus.
Wannan gargaɗi na zuwa ne bayan murabus ɗin Kwamishinan Sufuri, Alhaji Ibrahim Namadi, ya yi biyo bayan belin wani da ake zargin dilan miyagun ƙwayoyi, Sulaiman Danwawu.
Manoma sun koka kan rabon takin gwamnati a Sakkwato Hatsarin Mota: Yadda hanyar Lambata ke laƙume rayuka a NejaWannan lamari ya tayar da ƙura, wanda hakan ya sa Gwamna Abba, ya ɗauki mataki.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, gwamnan ya bayyana rashin jin daɗinsa kan lamarin.
Hakan ta sa ya jaddada buƙatar dukkanin mambobin majalisar da sauran manyan jami’an gwamnati su kasance masu gaskiya da riƙon amana.
“Ba za mu lamunci kowace irin ɗabi’a ta ƙashin kai da za ta ci gaba da lalata ƙimar gwamnatinmu ba,” in ji Gwamnan.
“Dukkanin ma’aikata dole su kasance masu lura da kuma ɗaukar nauyin ayyukansu. Ba ofishinku kawai kuke wakilta ba, kuna wakiltar gwamnatinmu.”
Gwamnan ya ƙara da cewa duk wanda ba zai iya sauke nauyin amanar da aka ɗora masa ba, ya yi murabus da kansa maimakon aikata wani abu da zai ɓata sunan gwamnati.
Ya kuma nanata cewa yaƙi da miyagun ƙwayoyi da sauran munanan ɗabi’u a cikin al’umma yana daga cikin ginshiƙin mulkinsa.
Ya ce duk wanda aka samu yana da hannu kai-tsaye ko a kaikaice wajen taimaka wa masu aikata irin waɗannan laifuka, zai fuskanci hukunci.
“Mun hau mulki da kyakkyawan manufa ta daidaita al’amura, gaskiya da ci gaba a Jihar Kano. Wannan buri ba zai taɓa taɓewa ba,” in ji shi.
Wannan mataki da gwamnan ya ɗauka na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar ta’ammali da miyagun ƙwayoyi ke ƙara barazana ga matasa da zaman lafiyar al’umma a jihar.
Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da adalci, gaskiya da kyakkyawan shugabanci ga al’ummar Jihar Kano.