Aminiya:
2025-11-04@14:04:07 GMT

Ministan Harkokin Wajen Iran ya isa taron Kungiyar OIC a Turkiyya

Published: 21st, June 2025 GMT

Wakilin ƙasar Iran ya isa birnin Santanbul na ƙasar Turkiyya domin halartar taron Ƙungiyar Haɗin kan Kasashen Musulmi (OIC) a ranar Asabar.

Kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ruwaito cewa, a yayin taron Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, zai gana da jami’an diflomasiyya na ƙasashen Larabawa don tattauna batun rikicin da ke ƙara ƙamari tsakanin ƙasarsa da Isra’ila.

Kimanin jami’an diflomasiyya 40 ne ake sa ran za su halarci taron a daidai lokacin da Isra’ila da Iran ke ci gaba da musayar hare-haren makamai masu linzami.

“Ministan harkokin wajen ya isa Istanbul a safiyar yau domin halartar taron ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan Musulunci,” in ji Tasnim.

Yadda Iran ta lalata cibiyar kimiyya mafi muhimmanci a Isra’ila Najeriya ta tura sojoji domin samar da zaman lafiya a Gambia

Wannan ziyarar ta zo ne bayan da Ministan ya gana da takwarorinsa daga Biritaniya, Faransa, da Jamus a Geneva a ranar Juma’a.

A cewar kamfanin dillancin labaran, “A wannan taron, bisa shawarar Iran, za a tattauna batun harin da gwamnatin Isra’ila ta kai wa kasarmu musamman,” in ji Araghchi.

Isra’ila ta fara farmakinta ne a safiyar 13 ga watan Yuni, tana mai cewa Iran tana dab da ƙera makaman nukiliya.

Wannan ya haifar da martani nan take daga Tehran, a rikici mafi mubi da aka taɓa fuskanta tsakanin kasashen biyu masu zaman doya da manja.

Tun da farko a ranar Juma’a, Araghchi ya bayyana cewa Iran a shirye take ta “sake duba harkokin diflomasiyya” idan har “aka dakatar da hare-haren Isra’ila.”

Ana sa ran ministocin ƙasashen Larabawa za su fitar da sanarwa bayan ganawarsu, in ji kamfanin dillancin labarai na ƙasar Turkiyya Anadolu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Iran Isra ila Ƙasashen Larabawa

এছাড়াও পড়ুন:

Gidan rediyo ya ɗauki nauyin sanya yara 40 a makaranta a Kano

Himma Radio, wani gidan rediyon al’umma da ke Jihar Kano, ya sanya yara 40 a makarantar firamare a ƙaramar hukumar Madobi.

An gudanar da bikin kaddamar da shirin ne a ranar Lahadi a harabar gidan rediyon da ke Madobi, da nufin rage yawan yara da ke gararamba a titunan jihar ba tare da zuwa makaranta ba.

An kashe ’yan bindiga 19 yayin wani hari a Kano Komai zai iya faruwa a hare-haren da za mu kai Nijeriya — Trump

Shugaban gidan rediyon, Ismail Yusuf Makwarari, ya ce wannan shiri wani ɓangare ne na aikin al’umma da gidan rediyon ke yi, kuma suna da burin faɗaɗa shi zuwa dukkanin ƙananan hukumomin jihar 44.

Ya ce, “Mu gidan rediyon al’umma ne da ke mayar da hankali kan harkar noma, kuma mun himmatu wajen inganta ci gaban yankunan karkara.

“Mun ƙaddamar da wannan shiri mai taken ‘Gangamin dawo da yara makaranta’ a matsayin wata hanya ta nuna cewa ilimi da noma su ne ginshiƙan ci gaba mai ɗorewa.”

Ya ƙara da cewa, “Mun zo da wannan tunani ne domin taimaka wa al’ummar da ke sauraron shirye-shiryenmu saboda Allah.

“A matsayina na shugaban kafar yaɗa labarai, mun ga cewa ba wai kawai mu riƙa fallasa matsalolin da ke cikin harkar ilimi ba ne, amma mu ma za mu iya taka rawa wajen kawo sauyi.”

Daga nan sai ya buƙaci sauran ƙungiyoyi da kamfanoni da su yi koyi da irin wannan aiki a matsayin gudummawarsu ga ci gaban ƙasa.

Hakimin Madobi kuma Majidadin Kano, Musa Saleh Kwankwaso, ya gode wa gidan rediyon bisa wannan hoɓɓasan da ya yi, tare da roƙon sauran masu hannu da shuni da su yi koyi da shi.

“Ilimi haƙƙin kowa ne, gwamnati ba za ta iya ɗaukar nauyin komai ita kaɗai ba. Irin waɗannan ƙungiyoyi da mutane su ma su shigo su taimaka. Muna farin ciki da wannan mataki da Himma Radio ta ɗauka,” in ji Hakimin.

Shugaban Jami’ar Bayero Kano (BUK), Farfesa Haruna Musa, wanda shi ma ya halarci bikin, ya ce Najeriya da ke da yawan jama’a sama da miliyan 200, waɗanda kuma fiye da rabinsu matasa ne, akwai buƙatar haɗa kai wajen tallafa wa fannin ilimi.

Ya kuma tabbatar da cewa ƙofar jami’arsa a buɗe take don haɗin gwiwa da duk masu ruwa da tsaki don ganin ta bunƙasa ilimi musamman a yankunan karkara.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kungiyar Hizbullah Ta yi Gargadin Mayar Da Martani Idan isra’ila Tayi Kokarin Kai Samame Ta Kasa
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Yayi Maraba Da Kalaman Da Hukumar IAEA Ta yi Kan Shirin Nukuliyarta
  • Barazanar kawo hari abin ɗaga hankali ne ga duk ’yan Nijeriya — Peter Obi
  • Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka
  • Gidan rediyo ya ɗauki nauyin sanya yara 40 a makaranta a Kano
  • Araqchi: Da Hadin Bakin Amurka, Gwamnatin Isra’ila ta kaddamar Da Hari Kan Kasar Iran
  • Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka
  • Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump
  • Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya
  • Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung