‘Yan Bindiga Sun Sace Dukkan Fasinjojin Motar Bas A Jihar Benuwe
Published: 23rd, June 2025 GMT
Rundunar ‘yansandan jihar Benuwe ta tabbatar da garkuwa da dukkan fasinjojin wata motar bas ta kamfanin Benue Links a hanyar Eke, Ugbokolo a karamar hukumar Okpokwu ta jihar a yammacin Lahadi. Wani ganau da ya zanta da LEADERSHIP ta wayar tarho, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 7 na yammacin ranar Lahadi, inda wasu ‘yan bindigar suka tare wata motar bas din da ta taho daga Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, suka yi awon gaba da fasinjojin da ke cikinta bayan sun kwace kayayyakinsu, sannan suka tafi da su cikin daji.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: jihar Benuwe
এছাড়াও পড়ুন:
An kashe matafiya biyu da yin garkuwa da uku a Kwara
Wasu ’yan bindiga sun kashe mutum biyu tare da yin garkuwa da wasu mutum uku a Ƙauyen Ganmu da ke kusa da Babanla a Ƙaramar hukumar Ifelodun a Jihar Kwara.
An samu rahoton cewa, harin ya faru ne a lokacin da waɗanda harin ya rutsa da su, ke kan hanyar Legas zuwa Babanla suka samu matsalar tayar motar a kusa da unguwar.
‘Hayakin janareta’ ya kashe mutum 4 ’yan gida daya a Borno Ana zargin ‘yan sanda da karya hannun SoworeA yayin da suke ƙoƙarin gyaran tayar ne wasu ’yan bindiga biyar suka yi musu kwanton ɓauna inda suka buɗe musu wuta.
Waɗanda aka kashe sun rasa rayukansu a harin, an bayyana sunayen su da: Alhaji Abdulrazak Ewenla ɗan ƙauyen Ajia da Jimoh Audu daga Gammu.
Mutanen ukun da aka sace sun haɗa da: Kazeem Ajide da Wahidi da Mufutau, duk da cewa har yanzu ba a tabbatar da sunayen mutanen biyu ba.
Bayan afkuwar lamarin, an tura tawagar jami’an ’yan sanda da sojoji da ’yan banga zuwa wurin da lamarin ya afku don tabbatar da tsaro tare da dawo da zaman lafiya.
Rundunar ’yan sandan jihar a cikin wata sanarwa da kakakinta, SP Adetoun Ejire-Adeymi ya fitar a ranar Alhamis, ta tabbatar da faruwar harin.
Sai dai ta yi watsi da wani faifan bidiyo da ke nuna cewa mazauna ƙauyen sun tsere, lamarin da ya haifar da tunanin an ƙauracewa garin.