Aminiya:
2025-06-25@15:28:36 GMT

Bello Turji ya kashe ’yan sa-kai sama da 40 a Zamfara

Published: 25th, June 2025 GMT

Daya daga cikin manyan ’yan bindigar da suka addabi Najeriya, Bello Turji ya kashe ’yan sa-kai sama da 40 a wani harin kwanton bauna da ya kai a jihar Zamfara ranar Lahadi.

Bayanai sun nuna daga cikin wadanda aka kashe din har da wasu jami’an hukumar tsaro ta DSS su hudu da kuma wani tubabben dan bindiga da yanzu yake aikin bayar da bayanai ga jami’an tsaro, Bashar Maniya.

Majiyoyi daga yankin sun tabbatar da cewa an kai harin ne a kusa da Rugar Chida, wani kauyen da mahaifin Bello Turjin ke rike da sarautar gargajiya.

Barau ya nesanta kansa daga masu nema masa kujerar mataimakin Tinubu a 2027 An tura ’yan China 6 kurkuku kan laifin ta’addanci a Nijeriya

An dai yi wa jami’an da ke tafiya a cikin motoci biyu da babura kwanton baunar ne a yankin wanda ya shafe mako biyu babu sabis din waya saboda aikin da sojoji suke a ciki.

Wata majiya a yankin ta tabbatar wa Aminiya cewa harin ya daga musu hankali matuka kuma an shirya shi yadda ya kamata.

Majiyar ta ce, “An mamaye su. Bello Turji da yaransa sun kashe mutum 40 daga cikinsu sannan suka kwace ababen hawan da suke kai.

“Turji ya ji dadin harin sosai musamman saboda Bashar Maniya na cikin wadanda aka kashe, wanda tun a baya dama babban abokin hamayyarsa ne kafin ya tuba daga ta’addancin,” in ji majiyar.

A cikin wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, an ga Bello Turji yana murna tare da nuna gawarwakin mutanen, ciki har da ta Bashar Maniya, yana rera wakokin cin nasara.

“Wannan ce gawar Kwamandan da ya jagoranci harin,” kamar yadda aka jiyo Turjin yana bayyanawa a cikin bidiyon.

Daga bisani dai an kwaso gawarwakin mutanen tare da gudunmawar sojojin sama, yayin da wadanda suka jikkata kuma aka garzaya da su asibiti.

Wani jami’in tsaro da bai amince a bayyana sunansa ba, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana shi da abin takaici da za a iya kauce masa matukar ana aiki tare tsakanin jami’an tsaro da mutanen gari.

Bayanai dai sun nuna gabanin kisan mayakan, an kashe ’yan bindiga yaran Bello Turji sama da 30 a wata ba-ta-kashi da aka yi tsakanin yaran Turjin da na Maniya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan sa Kai Zamfara

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan bindiga sun kashe ɗan sanda, sun jikkata wasu 3 a Zariya

Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai wa motar ’yan sanda hari a Zariya, inda suka harbe ɗaya daga cikinsu har lahira, tare da raunata wasu uku.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:30 na daren ranar Talata, a unguwar Dalan Waje da ke kan hanyar Galadimawa, a Ƙaramar Hukumar Zariya da ke Jihar Kaduna.

An ɗaure mutum 6 shekaru 120 kan satar yara a Kano Isra’ila da Iran sun ci gaba da musayar wuta duk da sanarwar tsagaita wuta

A cewar wani mazaunin yankin da ya shaida faruwar lamarin, motar ‘yan sandan na bin wata mota ƙirar Golf kafin a ji ƙarar harbe-harbe.

Nan take mutane suka fara kwanciya a ƙasa domin tsira da rayukansu.

Wannan hari ya girgiza mazauna yankin, inda suka ce ko da yake yankin ya daɗe yana fama da hare-haren ’yan bindiga, amma an daɗe ba samu hari ba.

A harin, an kashe wani ɗan sanda mai suna Nasiru Musa.

Ɗan sandan mazaunin ƙofar Kibo ne a cikin birnin Zariya.

Sauran da suka jikkata sun haɗa da direban motar ’yan sandan, Auwalu Hassan Ɗan Jos, wani ɗan-sa-kai mai suna Awwal Hassan, Iliyasu Ya’u da Salisu Mohammed.

An garzaya da su zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, Zariya, domin samun kulawar likitoci.

Da Aminiya ta tuntuɓi kakakin ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansur Hassan, ya ce yana wajen wani taron sanin makamar aiki, don haka bai da cikakken bayani.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan bindiga sun kashe ɗan sanda, sun jikkata wasu 3 a Zariya
  • Bejjo Turji ya kashe ’yan sa-kai sama da 40 a Zamfara
  • Gwamnatin Zamfara Ta Ƙaryata Rahoton Karɓo Lamuni Da Wata Jarida Ta Yaɗa
  • Harin asibiti ya kashe mutum 40 a Sudan — WHO
  • NNPC Ya Ƙara Kuɗin Fetur, Duba Sabon Farashin
  • Yanzu-yanzu: Zanga-zanga Ta Ɓarke A Jami’ar Neja Bayan Kashe Ɗalibi
  • Ina Da Isassun Kuɗi, Ban Ciwo Bashin Ko Kwabo Ɗaya Don Gyara Jihar Zamfara Ba – Gwamna Lawal
  • An kashe matar aure, manomi ya jikkata a wani sabon hari a Kaduna
  • Tinubu Ya Yi Allah-Wadai Da Harin Bam A Borno, Ya Yi Alhinin Fashewar Wani A Kano