Nazarin CGTN: Neman Kashe Kaso 5 Na GDP Kan Tsaro Ya Nuna Rashin Dabara Na NATO
Published: 25th, June 2025 GMT
Yaya girman neman fadadar kungiyar NATO yake? Alkaluma ne za su iya fayyacewa: Abun da aka kashe a duniya kan aikin soji a shekarar 2024 ya kai dala triliyan 2.72, inda kungiyar NATO ta dauki dala triliyan 1.5, wato kaso 55 na jimillar ta duniya.
Duk da rashin daidaiton karfin soji tsakanin kasashen duniya, NATO na ci gaba da sanya mambobinta su kara abun da suke kashewa a bangaren tsaro zuwa kaso 5 na alkalumansu na GDP.
Wani nazari da kafar CGTN ta gudanar ya nuna cewa, kaso 67.4 na wadanda suka bayar da amsa sun yi tir da yadda NATO ke gaggauta fadada karfinta na soji, suna gargadin hakan ka iya haifar da sabuwar takarar makamai da yin gagarumar barazana ga tsaro da kwanciyar hankalin duniya. Kana wasu kaso 80.4 na ganin akwai bukatar sa ido kan matakin na NATO.
Kafar CGTN ta kaddamar da nazarin ne a dandalinta na harsunan Ingilishi da Spaniyanci da Faransanci da Larabci da Rashanci, inda mutane 6000 daga kasashen waje suka bayyana ra’ayoyinsu cikin sa’o’i 12. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Najeriya ta yi watsi da sanya sunanta cikin jerin kasashen da ake tauye ’yancin addini
Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da matakin da Gwamnatin Amurka ta dauka na sanya sunan Najeriya cikin jerin “Kasashen Da Ake Tauye ’Yancin Addini” , wato jerin kasashen da ake zargi da take hakkin addini.
Ministan Yada Labarai da Al’adu, Mohammed Idris Malagi ne, ya bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja, inda ya ce matsalar tsaro da ake fuskanta a Najeriya ba ta shafi wani rukuni na addini ko kabila kai-tsaye ba.
Gwamnatin Tarayya ta fara shirin sayar da matatun manta ga ’yan kasuwa Hafsan sojin sama ya umarci a yawaita yi wa ’yan ta’adda ruwan bama-bamaiYa ce masu yada bayanan karya ne suka sa ake ganin kamar Najeriya tana nuna bambanci ta fuskar addini.
Malagi, ya ce gwamnati tana ci gaba da kokari wajen inganta harkar tsaro, sai dai ya bayyana cewa jami’an tsaro na wahala wajen isa wasu yankuna masu nisa a kan lokaci, don kai dauki.
Ya kara da cewa gwamnati na shirin dawo da tsarin tsaron al’umma domin tallafa wa rundunar tsaro ta kasa.
Da aka tambaye shi ko rashin nada jakadu ne ya haddasa wannan ce-ce-ku-ce da Amurka, Malagi ya ce dangantakar Najeriya da Amurka da sauran kasashe na tafiya daidai, kuma Shugaba Bola Tinubu na kokarin warware batun nada jakadu.
’Yan siyasar da suka fadi zabe ne ke yada labaran karya — AlakeA nasa bangaren, Ministan Harkokin Ma’adanai, Dele Alake, ya ce wasu ’yan siyasa da suka fadi a zabe ne ke yada labaran karya a Amurka cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya.
Ya gargade su da cewa irin wadannan maganganu na iya haddasa karin tashin hankali wanda zai iya shafar kowa, ba tare da la’akari da addini ba.
Keyamo ya karyata zarginShi ma Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya ce ikirarin Amurka karya ne, domin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba ta nuna wariyar addini.
Ya bayyana cewa yawancin manyan hafsoshin tsaro a Najeriya Kiristoci ne, sannan kuma Tinubu Musulmi ne matarsa Kirista, wacce malamar coci ce.
Keyamo, ya kara da cewa matsalolin tsaro a Najeriya suna shafar Musulmi da Kiristoci baki daya, don haka ya roki gwamnatin Amurka ta taimaka wajen yaki da ta’addanci maimakon dogaro da rahotannin karya.