CMG Ya Ja Hankulan Baki A Dandalin Tattaunawar Tattalin Arziki Na Kasa Da Kasa Na St. Petersburg Karo Na 28
Published: 22nd, June 2025 GMT
Daga ranar 18 zuwa 21 ga watan nan bisa agogon Rasha, an gudanar da dandalin tattaunawa tattalin arziki na kasa da kasa na St. Petersburg karo na 28 a kasar ta Rasha. Yayin taron, an sake gayyatar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG don halartar dandalin a matsayin abokin huldar yada labarai.
CMG, ya gina wani wurin baje koli mai zaman kansa a cikin wurin taron, da kafa dakin nuna shirye-shirye, da yin hira da manyan baki, kuma ya ba da rahotanni game da dandalin a cikin harsuna da yawa.
Ban da wannan kuma, a yankin baje kolin, an nuna sabon sakamakon aikace-aikacen fasahohin zamani na AI, wanda CMG ya yi nazari da kansa, da gabatar da shirye-shiryen CMG masu inganci da kuma kayayyakin al’adun kasa da kasa da ya kera da kansa, ya kuma jawo hankulan baki ‘yan siyasa da ’yan kasuwa da wakilan kafofin watsa labaru na kasashe daban-daban da suka halarci dandalin, inda suka tsaya tare da ziyartar dakin da ya kafa.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Najeriya na hasashen samun N300bn a shekara daga noman dabino
Gwamnatin Najeriya ta ce tana sa ran samun kimanin Naira biliyan 300 a duk shekara daga noman dabino a ƙasar.
Ta ce tana fatan samun wannan kuɗaɗen shiga ne daga rabon irin dabino guda miliyan biyar da ta samar ga manoma a wannan shekara ta 2025.
Darakta-Janar na Hukumar Yaƙi da Kwararowar Hamada (NAGGW), Alhaji Saleh Abubakar, ya ce, “Kowane iri ƙwaya ɗaya na iya samar da miliyan 100 na dabino, wanda kuɗinsa ya kai Naira miliyan ɗaya. Ga shi kuma sau biyu dabino ke yin ’ya’ya a shekara.
“Muna hasashen manoma za su samar da Naira biliyan 300, wanda tabbas zai bunƙasa tattalin arzikin Najeriya,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa hukumar za ta raba irin dabino miliyan biyar da ta samar ga jihohi 11 da ke maƙwabtaka da saharar hamada domin su ci gajiyar tattalin arzikin noman dabino.
Ya sanar da haka ne a yayin taron ƙaddamar sashen itatuwa a ƙauyen Maimalari da ke Ƙaramar Hukumar Yusufari ta Jihar Yobe.
A cewarsa, manufar shirin ita ce bunƙasa tattalin da ke cikin ɓangaren gandun daji wajen samar da ƙarin kuɗaɗen shiga da harkokin kasuwanci a jihohi takwas da ke gaɓar hamada.