Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice, ya sanya hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa da gidauniyar Milano Cortina 2026, wanda aka dorawa alhakin shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Milano Cortina ta shekarar 2026 dake tafe.

Yayin sanya hannu kan yarjejeniyar, sassan biyu sun amince su zurfafa hadin gwiwa a sassan yayatawa, da tsara ayyukan watsa gasar ta Olympics ta lokacin hunturu ta Milano Cortina, tare da aiwatar da musayar jami’ai.

Sakamakon wannan hadin-gwiwa, CMG ya samu ikon watsa gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Milano Cortina dake tafe a shekara mai zuwa a hukumance.

An kafa gidauniyar Milano Cortina 2026 a watan Disamban shekarar 2019, domin ya tsara, da tallata, da yayata harkokin wasanni, da na al’adu da za a gudanar karkashin gasar ta Olympics, da ajin gasar na masu bukata ta musamman. (Saminu Alhassan)

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

NAHCON ta ƙayyade N8.5m kafin alƙalami na kujerar Hajjin 2026

Hukumar NAHCON mai kula da sha’anin aikin Hajji a Nijeriya NAHCON, ta bayyana cewa an ƙayyade naira miliyan 8.5 a matsayin kafin alƙalami na kuɗin kujerar aikin Hajjin 2026.

NAHCON ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Alhamis, bayan gudanar da taro da shugabanni da kuma sakatarorin hukumomin aikin hajji na jihohin ƙasar.

An kashe mutum huɗu da tayar da ƙauyuka 17 a Sakkwato ’Yan sanda sun ƙwato jariri da aka sace a asibitin Ekiti

Mai magana da yawun NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta ce an ƙayyade ƙafin alƙalamin kuɗin kujerar domin fara shirye-shiryen ibadar ta wannan shekarar ta Musulunci.

Hajiya Fatima ta ambato shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, yana cewa an ƙayyade miliyan 8.5 ɗin ne a matsayin kafin alƙalami na aikin hajjin baɗi, kafin a kammala tattaunawa don sanin haƙikanin kuɗin.

Ya ce Saudiyya ta sake bai wa Nijeriya gurbin kujeru 95,000, kamar yadda ta samu a bara.

Farfesa Usman ya kuma yaba wa shugaba Bola Tinubu bisa irin goyon baya da yake bai wa hukumar da kuma alhazan Nijeriya.

A cewarsa, ƙoƙarin da gwamnatin tarayyar ta yi ne ma ya sa kamfanonin jirage suka amince suka karɓi biyan kuɗi da naira daga wajen alhazai a bara maimakon dala, domin saukaka musu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Barcelona Ta Tube Ter Stergen Daga Mukaminsa Na Kaftin Din Kungiyar 
  • NAHCON ta ƙayyade N8.5m kafin alƙalami na kujerar Hajjin 2026
  • An Bude Gasar Wasannin Ta Duniya Ta 2025 A Chengdu
  • Ta Yaya Za a Ba Matasa Damar Raya Kansu?
  • Tinubu Ya Taya Nafisa, Rukayya, Hadiza Murnar Samun Nasarar Zama Gwanaye A Gasar Turanci Ta Duniya
  • Shugaban IWGA: Birnin Chengdu Zai Karbi Bakuncin Gasar Wasanni Mafi Kyau A Tarihi
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce; Hadin Kai Tsakanin Cibiyoyi  Na Tabbatar Da Karfi Da Ci gaba
  • Buni ya shirya bikin karrama daliban da suka lashe gasar duniya
  • Ɗaliba ’yar shekara 15 daga Yobe ta lashe Gasar Muhawara ta Duniya
  • ’Yar shekara 17 daga Yobe ta lashe Gasar Turanci ta Duniya