Ina Da Isassun Kuɗi, Ban Ciwo Bashin Ko Kwabo Ɗaya Don Gyara Jihar Zamfara Ba – Gwamna Lawal
Published: 23rd, June 2025 GMT
Ya nanata cewa nasarar da aka samu ya zuwa yanzu ta samo asali ne sakamakon kyawawan tsare-tsare, ingantaccen jagoranci, da kuma kula da albarkatu.
Gwamnan ya bayyana cewa an samu ci gaba sosai a harkar tsaro a jihar idan aka kwatanta da abin da ya gada a shekarar 2023.
A cewar sa, inganta haɗin gwiwa da jami’an tsaro ya taka muhimmiyar rawa wajen rage yawaitar ayyukan ‘yan bindiga da sauran miyagun ayyuka a Zamfara.
Dangane da ababen more rayuwa kuwa, Gwamna Lawal ya ba da misali da ayyukan da ake ci gaba da aiwatarwa da kuma waɗanda aka kammala a ƙarƙashin shirin “Renewal Project,” wanda ya haɗa da gine-gine da gyaran hanyoyi, makarantu, da cibiyoyin kiwon lafiya a dukkanin ƙananan hukumomi goma sha huɗu na jihar.
Gwamna Lawal ya kuma bayyana shirin gwamnatin sa na bunƙasa fannin haƙar ma’adanai, inda ya bayyana shi a matsayin wani muhimmin fanni na bunƙasar tattalin arziki da ake samu a yanzu da aka samu daidaiton tsaro a jihar.
Da yake jaddada ƙudirin gwamnatin sa na tabbatar da gaskiya da riƙon amana da kuma tafiyar ci gaban al’umma, Gwamna Lawal ya nanata cewa duk nasarorin da aka samu ya zuwa yanzu an cimmasu ne ba tare da karbar rancen ko kobo ɗaya ba.
Ya kuma tabbatar wa da al’ummar jihar Zamfara cewa akwai wasu ayyukan ci gaba a nan gaba, domin gwamnatin sa ta ci gaba da mayar da hankali wajen ganin an samar da ci gaba mai ɗorewa da inganta rayuwar al’umma a faɗin jihar.
Da ya ke amsa tambaya dangane da rikicin PDP, Gwamna Lawal ya yi imanin cewa rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP ya wuce ɗan takarar ta na shugaban ƙasa a zaben 2023, Atiku Abubakar, kuma ya samo asali ne daga faɗan son rai a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar.
“Kowa yana da nasa batun; ba wai batun Atiku Abubakar ba ne, ya wuce shi,” inji shi.
“Matsala ce ta cikin gida a cikin PDP, kuma muna yin ƙoƙari sosai. Ina ganin abin ya shafi kishin mutane ne, kowa da kowa.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Gwamna Lawal ya
এছাড়াও পড়ুন:
An yi garkuwa da ɗan Majalisar Dokokin Jihar Filato
Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da ɗan Majalisar Dokokin Jihar Filato, mai wakiltar Mazaɓar Pankshin ta Kudu, Laven Denty Jacob.
A yammacin ranar Litinin aka yi garkuwa da shia gidansa da ke Anguwan Kagji, a Unguwar Dong, a Ƙaramar hukumar Jos ta Arewa.
Wani na kusa da shi ya tabbatar wa manema labarai cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 7:30.
A cewar mai taimaka wa ɗan majalisar, wasu mutane uku ne, da suka rufe fuskokinsu suka kai hari a ƙofar gidansa, a lokacin da suke jiran jami’an tsaronsa su buɗe kofar.
Ya bayyana cewa maharan sun ɗauke ɗan majalisar da ƙarfi daga cikin motarsa zuwa wani wuri, da ba a sani ba.
Ya ce masu garkuwar sun buqaci iyalansa su a biya su, kuɗin fansa naira miliyan hamsin.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred da Shugabannin Majalisar Jihar, har yanzu ba su ce komai ba, kan wannan al’amari.