Aminiya:
2025-08-06@09:24:07 GMT

’Yan Najeriya da suka maƙale a Isra’ila na neman ɗauki

Published: 21st, June 2025 GMT

’Yan Najeriya mazauna ƙasar Isra’ila sun maƙale bayan ɓarkewar yaƙin Iran da Isra’ila. Sun nemi agajin Gwamnatin Tarayya game da kan halin ƙuncin da suka faɗa tun bayan ɓarkewar yaƙi.

Cikin wani rahoto da Jaridar Punch ta wallafa, ’yan Najeriyar sun zargi gwamnati da rashin kai masu ɗauki yadda da ya kamata, inda suka ce tuni sauran ƙasashe suka fara kwashe ’yan ƙasarsu.

Rahoton ya bayyana cewa ’yan Najeriyar sun fi yawa a birnin Ƙudus da Tel Aviv, inda Iran ta tsananta kai hare-hare.

A halin yanzu, mazauna Isra’ilar sun bayyana cewa suna ɓoye ne a wurare da babu tabbas kuma rayuwarsu na cikin haɗari, a koyaushe komai na iya faruwa da su.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan Najeriya Iran Isra ila Najeriya

এছাড়াও পড়ুন:

Kotu ta hana jagoran adawa Maurice Kamto takarar shugaban ƙasa a Kamaru

Kotun tsarin mulkin Kamaru ta haramta wa jagoran adawar ƙasar, Maurice Kamto tsayawa takarar shugaban ƙasa, a babban zaɓe mai zuwa na watan Oktoba, kan abin da ta bayyana rashin cika ka’idojin tsayawa takara.

Lauyansa, Hippolyte Meli Tiakouang ne ya tabbatar wa manema labarai hukuncin kotun wanda ba za a iya ƙalubalanta ba, bayan kammala zamanta na wannan Talata.

A cewarsa, kotun ta yi watsi da ƙarar da suka shigar kan matakin hukumar zaɓen ƙasar na cire shi daga cikin jerin ’yan takarar da za su fafata a zaɓen ranar 12 ga watan Oktoban bana.

Mulkin Tinubu ya fi na Buhari muni — Maina Waziri ’Yan gida ɗaya sun kitsa garkuwar ƙarya domin karɓar N5m a wurin mahaifinsu

Mista Kamto mai shekaru 71, ya yi ƙaurin suna wajen sukar gwamnatin shugaba Paul Biya, kuma shi ne ya yi na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2018, bayan tsayawa takara a jam’iyyar MRC.

A wannan karo kuma ya nemi tsayawa takarar a jam’iyyar MANIDEM, inda ya bayyana muradin tsayawar watanni biyar da suka gabata.

Hukumar zaɓen ƙasar ta yanke hukuncin cire Kamto saboda “’yan takara masu yawa,” bayan wani ɗan takara daga wani tsagin jam’iyyar ya miƙa buƙatar makamanciyar wannan, wanda ya sa ake nuna damuwa kan halascin shugabancin jam’iyyar.

Bayan gabatar da hukuncin, Kamto wanda da alama bai ji daɗin hakan ba, ya fice daga harabar kotun ba tare da magana da ’yan jarida ba.

Hukuncin da aka yanke a ranar Talata ya ƙara tayar da fargabar hargitsi.

An jibge jami’an tsaro a kusa da cibiyar taro da ke babban birnin ƙasar, Yaoundé, inda Kwamitin Kundin Tsarin Mulki ya bayyana hukuncin, da kuma manyan titunan birnin.

A ranar da ta gabata, ’yan sanda sun harba hayaƙi mai sa hawaye tare da kama mutane da dama da suka fito zanga-zangar goyon bayan Kamto.

Lauyoyinsa waɗanda ba su yi ƙarin bayani kan mataki da za su ɗauka ba, sun ce Kamto ne zai bayyana matakin da zai ɗauka.

Masu suka na ganin cewa akwai wata maƙarƙashiya ne na kawar da ɗan siyasar daga zaɓen.

Duk da raɗe-raɗin rashin lafiya, yanzu haka shugaba Paul Biya mai shekaru 92, wanda ya shafe tsawon shekaru 43 yana mulkin Kamaru, zai sake neman wa’adi na takwas a kan karagar mulki ba tare da wata ƙwaƙƙwarar adawa ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kotu ta hana jagoran adawa Maurice Kamto takarar shugaban ƙasa a Kamaru
  • Wulayati: Iran Zata Mayar Da Martani Kan Gwamnati Da Ke Neman Yin Amfani Da Hanyar Zangezur Ta Hanyar Da Bata Dace Ba
  • Ɗaruruwan Tsaffin Jami’an Tsaron Isra’ila Sun Roki Trump Ya A Dakatar Da Yakin Gaza
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Ayyuka Suka Ragu A Jihohi Bayan Kudin Shiga Ya Karu
  • Malamai A Najeriya Suna Goyon Bayan Iran A Yadda Take Fuskantar HKI
  • Iran Ta Ce Ba Wani Ma’aikacin Hukumar IAEA A Kasar A Halin Yanzu
  • Ƴan matan Najeriya Sun Lashe Gasar Kwallon Kwando Ta Afirka
  • Dangote Ya Ɗauki Nauyin Bikin Baje Kolin Gidajen Afrika Da Mahalarta Ƙasashe 21
  • Sojoji sun ceto malamin Jami’a da aka sace a Taraba
  • Sai an samar da ’yantacciyar ƙasar Falasɗinu za mu ajiye makamai — Hamas