Najeriya ta tura sojoji domin samar da zaman lafiya a Gambia
Published: 21st, June 2025 GMT
Najeriya ta tura sojojinta 197 domin zuwa aikin tabbatar da tsaro da wanzar da zaman lafiya a kasar Gambia.
Dakarun na Najeriya waɗanda tuni suka kammala samun horo, za sai yi aikin wanzar da zaman lafiya a Gambia be a ƙarƙashin rundunar Ƙungiyar Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) da sunan (ECOMIG).
Shugaban Ayyuka na Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya, Manjo-Janar Uwem Bassey, ya buƙaci sojojin da su kasance masu nuna nuna ƙwarewa da jarumta a yayin gudanar da ayyukansu a ƙasar Gambia.
Ya yi wannan kira ne a jawabinsa a wurin bikin yaye sojojin a Barikin Sojoji na Jaji da ke Jihar Kaduna, kafin tafiyarsu.
Yadda Iran ta lalata cibiyar kimiyya mafi muhimmanci a Isra’ila An sallami ƙarin ma’aikata 639 a tashar Muryar AmurkaManjo-Janar Bassey ya buƙaci sojojin da su guji nuna son kai, su mutunta hakkokin ɗan Adam da kuma dokoki da al’adun al’ummar Gambia.
Ya gargaɗe su game da cin zarafi musamman na jinsi, tare da cewa duk sojan aka samu da laifi zai gamu da tsauraran matakan ladabtarwa.
Bassey ya bayyana cewa Najeriya tana da dogon tarihi na bayar da gudummawa ga ayyukan wanzar da zaman lafiya na ƙasar da ƙasa, inda sojojinta ke samun karɓuwa a duniya saboda jaruntakarsu, da ƙwarewarsu.
Sojojin Najeriya sun taka muhimmiyar rawa wajen dawo da zaman lafiya a rikice-rikicen da aka samu a faɗin Afirka da ma duniya, ciki har da Lebanon da Yugoslavia da Laberiya, Saliyo, da Sudan, inda suka ci gaba da samun yabo saboda jaruntakarsu da ƙwarewarsu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Najeriya Sojojin Najeriya wanzar da zaman lafiya Zaman lafiya da zaman lafiya a
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Isra’ila Sun Kashe Falasɗinawa A Wurin Rabon Abinci A Gaza
Rahotanni daga Gaza na cewa sojojin Isra’ila sun sake buɗe wuta kan Falasɗinawa da ke cikin tsananin buƙatar agaji a kusa da inda ake rabon kayan tallafi a cibiyoyi biyu, a jiya Lahadi.
Asibitoci a Gaza sun ce aƙalla Falasdinawa 27 aka kashe.
Rahotanni na cewa sojojin sun buɗe wa mutane wuta bayan isa gab da ɗaya daga cikin cibiyoyin rabon agajin na gidauniyar da Amurka da Isra’ila ke mara wa baya a Rafah.
Sanan sauran kuma an kashe su ne a sansanin da ke tsakiyar Gaza.
Har yanzu sojojin Isra’ila ba su yi martani ba kan wannan rahoton.
Hamas ta ce ƙungiyar agaji ta Red Cross kaɗai za ta iya miƙa wa ‘yan Isra’ilar da take riƙe dasu a Gaza idan har aka cimma daidaituwar ba da dama a shigar da kayan agaji a duk sassan zirrin.