Aminiya:
2025-11-03@01:57:26 GMT

Za mu iya galaba kan Iran ko babu Amurka — Isra’ila

Published: 20th, June 2025 GMT

Shugaban Isra’ila, Isaac Herzog, ya bayyana cewa ƙasarsa za ta iya samun nasara a yaƙin da take yi da Iran ko da kuwa Amurka ba ta shigar mata ba.

Sai dai Herzog ya shaida wa ABC News cewa kawar da barazanar nukiliyar Iran yana da muhimmanci ga “duniya mai ’yanci”, ciki har da Amurka.

Nan da mako biyu za mu yanke shawara kan shigar wa Isra’ila yaƙi — Trump Muna shawartar Trump kada ya shiga yaƙin Iran da Isra’ila — Birtaniya

Da yake amsa tambayar ko me zai ce dangane da yiwuwar shigar wa ƙasarsa yaƙin da take yi da Iran da Shugaba Donald Trump ya yi iƙirari, Herzog ya ce “ina da cikakkiyar yarda a kan duk wani hukunci da zai yanke kuma ina da tabbacin duk abin da ya yanke shi ne daidai.

Herzog ya ce mako guda ke nan da fara yaƙin amma ya tabbatar da cewa barazanar Iran ba za ta kau ba nan take.

“Babbar nasarar da za mu samu ita ce kawo ƙarshen barazanar nukiliyar Iran,” a cewar Herzog.

“[Jagoran addini na Iran, Ayotallah Ali Khamenei] shi ne kan macijin da ke jagorantar duk wata barazana da Iran take yi da muke buƙatar mu sare.

“Tun ba yanzu ba yake babatun ganin bayan ƙasarmu da al’ummarta. Saboda haka ba mu da wata manufa a yanzu face mun yi maganinsa,” kamar yadda Herzog ya shaida wa gidan talabijin na ABC.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Benjamin Netanyahu Iran Isaac Herzog

এছাড়াও পড়ুন:

Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon barazana — Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan kalaman da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi game da Najeriya.

Kwankwaso, ya yi wannan magana ne bayan Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin yaƙi game da zargin kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci.

Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da Amurka

A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso, ya ce Najeriya ƙasa ce mai cikakken ’yanci, wadda ke fama da matsalar tsaro daga miyagu a sassa daban-daban na ƙasar.

“Matsalar tsaron da muke fuskanta ba ta bambanta tsakanin addini, ƙabila ko ra’ayin siyasa,” in ji shi.

Ya buƙaci gwamnatin Amurka da ta tallafa wa Najeriya da sabbin fasahohi domin yaƙar matsalar tsaro maimakon yin kalaman da za su iya raba kan ’yan ƙasa.

“Amurka ya kamata ta taimaka wa hukumomin Najeriya da ingantattun fasahohi don magance matsalolin tsaro, maimakon yin barazanar da za ta ƙara raba ƙasar,” in ji Kwankwaso.

Haka kuma, ya shawarci Gwamnatin Najeriya da ta naɗa jakadu na musamman domin inganta hulɗar diflomasiyya da Amurka da kare muradun ƙasar a matakin duniya.

Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su zauna lafiya, inda ya bayyana cewa wannan lokaci ne da ya dace a fifita haɗin kan ƙasa ba abin da ke raba ta ba.

“Wannan lokaci ne da ya kamata mu mayar da hankali kan abin da zai haɗa kanmu ba wanda zai raba mu ba. Allah Ya albarkaci Najeriya,” in ji shi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba
  • Fursunan da aka yanke wa hukuncin kisa ya tsere daga gidan yari a Yobe
  • Tinubu ya yanke hulɗa da Amurka kawai — Sheikh Gumi
  • Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon barazana — Kwankwaso
  • Araqchi: Da Hadin Bakin Amurka, Gwamnatin Isra’ila ta kaddamar Da Hari Kan Kasar Iran
  • Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka
  • Barazanar Amurka Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya: Tinubu Da Trump Za Su Gana Kwanan Nan — Bwala
  • IAEA : Babu wata shaida da ke nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya
  • Jamus ta shiga sahun ƙasashen da ke neman kawo ƙarshen yaƙin Sudan
  • Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya