Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya bayyana cewa, shugaban kasar Xi Jinping, zai halarci bikin tunawa da cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin kin jinin harin sojojin Japan, da yakin kin tafarkin murdiya, da safiyar ranar 3 ga watan Satumban bana, tare da gabatar da jawabi. Kazalika a ranar, kasar Sin za ta gudanar da gagarumin bikin faretin soja a filin Tian’anmen dake nan Beijing, inda shugaba Xi zai duba faretin.

(Amina Xu)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

DSS ta yi wa Malami tambayoyi kan harin da aka kai masa a Kebbi

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi wa tsohon Ministan Shari’a kuma Antoni-Janar na Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami, tambayoyi a kan harin da aka kai wa ayarin motocinsa a Jihar Kebbi.

An gudanar da tambayoyin ne a ofishin hukumar na Birnin Kebbi a ranar Litinin, inda Malami ya bayyana cewa an yi masa tambayoyin cikin ƙwarewa da mutuntawa.

A ranar 1 ga Satumba, 2025 ne aka kai wa ayarin motocin da ke rakiyar Malami hari a Birnin Kebbi, bayan ya dawo daga gaisuwar ta’aziyya ga iyalan marigayi Babban Limamin Masallacin Dakta Bello Haliru Jumu’a.

Shaidu sun bayyana cewa an lalata motocin rakiyarsa kusan guda 10, sannan da dama daga cikin magoya bayansa sun jikkata.

Burkina Faso, Mali da Nijar sun fice daga Kotun ICC ’Yan sanda sun kama mutum 4 kan kai wa Lakurawa babura a Kebbi

Malami ya yi zargin cewa harin yana da nasaba da siyasa, duk da cewa jam’iyya mai mulkin jihar — APC, ta nesanta kanta daga lamarin.

Daga bisani Malami ya shigar da ƙorafi zuwa ga hukumomin tsaro, ciki har da ’yan sanda da DSS.

A wani jawabi da ya wallafa a shafinsa na Facebook da yammacin Litinin, Malami ya ce an gudanar da binciken cikin gaskiya da ƙwarewa, tare da nuna masa mutuntawa.

“Na tabbatar cewa DSS ta gayyace ni domin bayar da gudunmawa wajen binciken harin da aka kai mini da ’yan rakiyata a Kebbi a ranar 1 ga Satumba, 2025.

“Ƙorafin ya samo asali ne daga manyan ’yan adawa a jihar. Ina yaba wa hukumar DSS bisa yadda suka gudanar da binciken cikin gaskiya da mutunci.

“An yi min tambayoyi cikin mutuntawa, kuma zan ci gaba da bayar da haɗin kai don tabbatar da kammala binciken yadda ya kamata,” in ji shi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Imam Khamenei: Hadin kan al’ummar Iran a yakin kwanaki 12 ya sanya makiya kunya
  • An Yanke Wa Sojojin Da Suka Sayar Wa ‘Yan Ta’adda Makamai Hukuncin Ɗaurin Rai-da-rai A Borno
  • Xi Jinping Zai Halarci Bikin Murnar Cika Shekaru 70 Da Kafuwar Yankin Xinjiang Na Uygur Mai Cin Gashin Kansa
  • DSS ta yi wa Malami tambayoyi kan harin da aka kai masa a Kebbi
  • CORET Ta Yaba Da Nasarar Shirin Ciyarda Daliban Makarantun Makiyaya
  • An gudanar da bikin ɗaga tutar Falasɗinu a Birtaniya
  • Kasar Sin Za Ta Shirya Taron Mata Na Duniya A Beijing Yayin Cika Shekaru 30 Da Taron Mata Na 1995
  • Xi Jinping Ya Mika Gaisuwar “Bikin Girbi Na Manoman Kasar Sin” Na Takwas
  • Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Aiwatar Da Kisan Gilla Kan Fararen Hula 5 A Kudancin Kasar Lebanon
  • Hizbullah Ta Gayyaci Mutane Da Su Fito Domin Tunawa Da Zagayowar Shahadar Sayyid Hassan Nasrallah