Iran: Amurka ta ɗebo ruwan dafa kanta
Published: 23rd, June 2025 GMT
Manyan Hafsoshin Tsaro na ƙasar Iran sun sha alwashin mayar wa Amurka da martani mai tsanani wanda sai ta yi da-na-sanin harin da kai wa Iran.
Rundunar Tsaro ta Iran ta sanar da haka ne bayan wani zama da Babban Kwamandan Sojojin ƙasar, Amir Hatami, ya yi da wasu manyan kwamandojinsa.
Harami ya shaida wa taron tsare-tsaren cewa ya zama tilas Amurka ta girbi abin da ya shuka a Iran a wannan karon.
Ya bayyana cewa ko a baya, Iran ta saba koya wa Amurka darasi a duk lokacin da ta takali Iran.
Koriya ta Arewa za ta taimaka da gyara tashoshin nukiliyan Iran —Masani NAJERIYA A YAU: Matakan daƙile kisan matafiya a hanyoyin NajeriyaBabban Hafsan Tsaron Iran, Abdolrahim Mousavi, a cikin wata sanarwa, ya ce, Iran ba za ta taɓa ja da baya ba, duk abin da Amurka za ta yi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Iran
এছাড়াও পড়ুন:
Yada labaran karya a intanet babban laifi ne a Musulunci – Sheikh Ibrahim Khalil
Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya gargadi masu yada labaran karya musamman a kafafen sada zumunta da su daina, domin Musulunci ya haramta hakan.
Ya bayyana cewa a Musulunci, yada labaran karya daidai yake da yin karya, kuma addinin Musulunci yana tsananin kin masu karya.
UNGA: Yau Shettima zai gabatar da jawabin Najeriya a MDD Kotun Indiya ta daure dan Najeriya shekara 10 kan safarar miyagun kwayoyiSheikh Khalil ya fadi hakan ne a Kano a ranar Talata yayin wani taron horaswa na kwanaki biyu da aka shirya wa malamai da limamai kan yadda za a yaki labaran karya da kuma inganta fahimtar kafofin yada labarai, wanda kungiyar Alkalanci ta shirya, wata kungiya da ke tantance gaskiyar labarai da ilmantar da jama’a.
A cewar malamin, “Musulunci ya riga ya haramta yin karya, kamar yadda Allah ya gargade mu a cikin Alkur’ani: ‘Kada ku bi abin da ba ku da ilimi a kansa. Hakika kunne, ido da zuciya, duk abubuwan tambaya ne a gare ku’.
“Saboda haka, kirkira da yada labaran karya ba su da bambanci da yin karya, wanda laifi ne,” in ji shi.
Ya kara da cewa malamai na da muhimmiyar rawa da za su taka wajen ilmantar da jama’a game da hadarin yada labaran karya, musamman a intanet da kafafen sada zumunta.
Tun da farko da yake jawabin maraba, Editan Alkalanci kuma wanda ya shirya taron, Alhassan Bala, ya jaddada muhimmancin shirya bitar ga malaman.
“Muna rayuwa a wani zamani da bayanai ke yaduwa cikin sauri fiye da da. Abin takaici, yawancin abin da ake yadawa yana da rudani, raba kan jama’a, kuma yana da illa,” in ji shi.
Bala ya bayyana cewa an tsara taron musamman don malamai saboda tasirinsu a cikin al’umma.
“Wa’azinku da koyarwarku suna da tasiri wajen gina ra’ayin jama’a. Tare da wannan amana, akwai nauyin tabbatar da cewa abin da kuke yadawa gaskiya ne, an tabbatar da shi, kuma yana da amfani,” kamar yadda ya fada wa mahalarta bitar.
Ya ce tun bayan kafuwarta a watan Oktoban bara, kungiyar Alkalanci ta mayar da hankali kan yaki da labaran karya da ake yadawa da Hausa, tare da niyyar fadada ayyukanta a fadin Najeriya.
Ya jaddada cewa har manyan shugabanni da ake girmamawa na iya yada karya ba tare da sun sani ba, lamarin da ke nuna muhimmancin tunani mai zurfi da tabbatar da gaskiya.
A yayin bitar an koya wa mahalarta amfani da fasahohin zamani wajen tantance gaskiyar rubuce-rubuce, hotuna da bidiyo, da nufin yaki da yada labaran karya.
Taron ya kuma yi kira ga ci gaba da hadin gwiwa tsakanin shugabannin addini da masu wayar da kan jama’a don kare gaskiya da hadin kai a cikin al’umma.