Aminiya:
2025-09-24@11:12:26 GMT

Matsayi ya yi maraya ɗan shekara 10 kisan gilla a Zariya

Published: 23rd, June 2025 GMT

Ana zargin wani ɗan shekaru 18 da kashe wani maraya ɗan shekara 10 a yankin Ƙaramar Hukumar Zariya ta Jihar Kaduna.

’Yan sanda sun kama matashin ne kan zargin sa da yi wa ɗan yaron, wanda ɗan baffansa ne, ɗaurin goro tare da azabtar da shi saboda yaron ya ƙi amincewa ya yi lalata da shi.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da ta gabata a unguwar Iyan Juma da ke Karamar Hukumar Zariya.

Mahaifiyar marigayin mai suna Asama’u Mohammed ta shaida wa Aminiya cewa, “Na dawo wajen aikatau kamar yadda na saba yi don na samo abin da zan ba su su ci tare da ’yan uwansa, sai ga yayansa ya shigo a guje ya ce ga Idris can a kwance cikin jini kuma fuskarsa a kumbure, wai sun yi faɗa da wani duk an ji mishi ciwo, nan da nan na yafa hijabi ni da ɗan uwar gidana muka tafi inda yake.”

Aminiya ta garzaya Babban Ofishin ’yan sanda da ke Ƙofar Fada cikin birnin Zariya domin ji daga bakin babban jima’i, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya shaida wa wakilinmu, cewa sun tattara bayanai yadda lamarin ya kasance kuma sun tura zuwa babban ofishinsu da ke Kaduna

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kaduna DSP Mansur Hassan ya tabbatar wa wakilin namu da faruwar lamarin, da kama wanda da ake zargi.

Ya ƙara da cewa bayan sun kammala bincike za su tora zuwa kuto.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Sarkin Ruman Katsina ya rasu

A yau Litinin Allah Ya yi wa Sarkin Ruman Katsina kuma Hakimin Batsari, Alhaji Tukur Ma’azu, rasuwa.

Marigayin, wanda ya shafe shekaru 74 a duniya, ya daɗe yana fama da jinya gabanin rasuwarsa.

Hisbah ta kama masu safarar mata zuwa Saudiyya a Kano Jariri ya mutu a bayan uwarsa yayin tsere wa ’yan bindiga a Neja

Alhaji Tukur wanda ya shafe shekaru 43 yana riƙe da sarautar Hakimin Batsari, ya rasu ya bar mata biyu, ’ya’ya da kuma jikoki.

Za a gudanar da jana’izarsa da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin yau a gidansa da ke cikin garin Batsari, kamar yadda sanarwa daga iyalansa ta tabbatar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kotun Indiya ta daure dan Najeriya shekara 10 kan safarar miyagun kwayoyi
  • An kama ɗan sandan bogi a Kano
  • An ƙona al’aurar ’yar shekara 5 saboda fitsarin kwance a Bauchi
  • An ƙone al’aurar ’yar shekara 5 saboda fitsarin kwance a Bauchi
  • Mahara sun kashe ɗan sanda, sun ɗauke bindigarsa a Taraba
  • Sarkin Ruman Katsina ya rasu
  • Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Aiwatar Da Kisan Gilla Kan Fararen Hula 5 A Kudancin Kasar Lebanon
  • Yadda Ƴan Agbero’ Ke Cin Karensu Ba Babbaka A Abuja
  • Babu Wanda Ya Jawo Ra’ayina  Zuwa Masana’antar Kannywood —Umar Hassan (2)
  • An Cafke Wani Magidanci Da Lafin Sojan Gona A Katsina