Aminiya:
2025-09-24@15:45:14 GMT

EFCC ya kama manyan jami’an NNPC kan badaƙalar Dala 7.2bn

Published: 24th, June 2025 GMT

Hukumar EFCC mai yaki da masu karya tattalin arziki ta tsare wasu tsofafin manyan jami’an Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) kan zargin badakalar kudade da yawansu ya kai Dala biliyan 7.2.

Jami’an EFCC sun tsare tsohon Babban Jami’in Kudi na NNPCL, Umar Ajiya Isah da kuma tsohon Manajan-Daraktan Matatar Mai ta Warri, Jimoh Olasunkanmi, kan zargin almundahanar.

Wani babban jami’in EFCC da ya nemi a boye sunansa ya ce hukumar ta tsare tsoffin manyan jami’an na NNPC ne kan zargin wadaka da kudaden gyaran matatun mai da ke Kaduna da Warri da kuma Fatakwal.

Wakilinmu ya yi kokarin samun karin haske daga kakakin EFCC, Dele Oyewale, amma jami’in bai amsa duk kiraye-kirayen da aka yi masa da kuma rubutattun sakon da aka tura masa domin samun bayani a hukumance.

Umar Ajiya ya kasance mai kula da harkokin kula da kudaden gyaran matatun guda uku da kuma da kuma manyan jami’an da ke aiki.

Iran ta kama ’yan leƙen asirin Isra’ila 6 Iyalan Kanawa da aka kashe a Uromi sun zargin gwamnati da yin watsi da su

Wani jami’in EFCC ya bayyana cewa hukumar tana kuma bincikar was jami’an NNPC da ke kula da wasu muhimman ayyuka kan zargin su da karkatar da kudade da kuma karbar na-goro daga ’yan kwangila.

A cewarsa, wadanda binciken ya shafa sun hada da Manajan-Daraktan Matatar Warri, Tunde Bakare; tsohon Manajan-Daraktan Matatar Fatakwal, Ahmed Adamu Diko da wani tsohon Manajan-Daraktan matatar, Ibrahim Monday Onoja.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan kwangila Matatar mai Manajan Daraktan manyan jami an

এছাড়াও পড়ুন:

NAJERIYA A YAU: Abin Da Doka Ya Ce Kan Kisan Jami’an ‘Yan Sanda

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Kisan jami’an tsaro na cigaba da zama ruwan dare a Najeriya, lamarin da ya daɗe yana tayar da hankali, amma a ‘yan kwanakin nan abin ya ƙara muni.

 

Misali, kwanan nan a an kashe wasu jami’an ‘yan sanda a kananan hukumomin Katsina-Ala da Ukum a jihar Benue, inda ‘yan bindiga suka kai hari tare da kashe ‘yan sanda uku inda suka kuma sace wasu bakwai.

NAJERIYA A YAU: Yadda Wata Bakuwar Cuta Take Cin Naman Jikin Mutanen Malabu DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan abin da dokokin kasa suka ce kan kisan jami’an ‘yan sanda.

Domin sauke shirin, latsa nan

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jami’an Tsaron Amruka Sun Kai Hari Ofishi Da Gidan John  Bolton
  • An Kama Tsohon Ɗan Wasan Super Eagles, Victor Ezeji, Kan Zargin Aikata Zambar ₦39.8m
  • UNGA: Shettima Ya Tallata Damar Zuba Jari Na Dala Biliyan 200 A Fannin Makamashi A Nijeriya
  • NAJERIYA A YAU: Abin Da Doka Ya Ce Kan Kisan Jami’an ‘Yan Sanda
  • CAC ta soma yi wa kamfanoni rijista da fasahar AI
  • Ballon d’Or: Wa zai lashe kyautar 2025?
  • Ballon d’Or: ’Yan wasa 5 da ke iya lashe kyautar 2025 
  • An kashe jami’an tsaro 53 a cikin mako biyu —Bincike
  • APC Da PDP Na Zargin Juna Kan Amfani Da Addini Wajen Neman Nasara A 2027
  • Yadda Wasu Mata Ke Gwada Mazansu Ta Hanyar Magana Da Su Ta Wasu Hanyoyi Don Sanin Ku Suna Kula Mata