Gwamnatin Kano ta ba da hutun sabuwar shekarar musulunci
Published: 26th, June 2025 GMT
Gwamnatin Kano ta ayyana gobe Alhamis, 26 ga watan Yunin 2025, a matsayin hutun rana daya na sabuwar shekarar musulunci ta 1447.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da ofishin shugaban ma’aikatan Kano ya fitar a yammacin wannan Larabar.
Gwamnatin Gombe za ta biya ’yan fansho Naira biliyan 6.6 kuɗin ritaya Arsenal za ta ɗauki ɗan ƙwallon Brentford Christian NorgaardSanarwar wadda babban sakatare a ofishin shugaban ma’aikatan, Ashiru Abdullahi ya fitar, ta bukaci ma’aikatan jihar da su yi amfani da wannan dama domin yi wa jihar da kuma kasa baki ɗaya addu’ar zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa.
Aminiya ta ruwaito Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, a jiya Talata yana ba da umarnin fara duban watan Muharram na sabuwar shekarar musulunci ta 1447 daga yau Laraba, 29 ga watan Zulhijjan 1446.
Kawo yanzu Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Islama da Sarkin Musulmin ke jagoranta ba ta sanar da ganin jinjirin watan na Muharram ba.
Sai dai kuma a yau din aka samu rahoton ganin watan sabuwar shekarar musulunci ta 1447 Bayan Hijira a Saudiyya.
Cikin wani saƙo da shafin Haramain na Saudiyya ya wallafa ya ce an ga watan da maraicen yau Laraba, 25 ga watan Yuni.
Hakan na nufin shekarar 1446 ta zo ƙarshe wannan rana a ƙasar ta Saudiyya, inda goben za ta kasance 1 ga Muharamm, watan farko a kalandar musulunci.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Kano Muharram Sabuwar shekara sabuwar shekarar musulunci
এছাড়াও পড়ুন:
An buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarawaba a Katsina
Hukumar kula da makarantun firamare da sakandare ta Jihar Katsina ta sanar da sake buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarabawar zangon farko na shekarar karatu.
A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Sani Danjuma Suleman, ya fitar a madadin Shugaban hukumar, ta ce makarantun firamare, sakandiren je-ka-ka-dawo da kuma makarantu masu zaman kansu za su buɗe daga yau Talata domin ci gaba da jarabawar zangon farko.
Sanarwar ta ƙara da cewa, sauran makarantun kwana za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai lokacin da hali ya ba da dama.
Aminiya ta ruwaito cewa, a bayan nan ne Gwamnatin Katsina ta rufe makarantun bayan ƙaruwar hare-haren sace ɗalibai da masu garkuwa da mutane suka sake farfaɗowa da su a wasu yankuna.
Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne da nufin daƙile matsalar tsaro da kuma sa ido a kan al’amura.
A ƙarshe, hukumar ta roƙi haɗin kan iyaye da masu kula da ɗalibai domin su ci gaba da ba wa shirin goyon baya tare da ƙarfafa ɗaliban su dage da karatu wajen rubuta jarabawar da suke yi.