Harin asibiti ya kashe mutum 40 a Sudan — WHO
Published: 24th, June 2025 GMT
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce sama da mutane 40 ciki har da ma’aikatan kiwon lafiya aka kashe a harin da aka kai wani asibiti da ke Sudan a ƙarshen mako.
Ofishin hukumar ta WHO da ke Sudan, ya ce daga cikin waɗanda suka mutu akwai ƙananan yara shida da jami’an kiwon lafiya biyar, sannan kuma an yi wa ginin asibitin mummunar ɓarna.
RFI ya ruwaito cewa an dai kai harin ne kan Asibitin Al Mujlad da ke a yammacin Kordofan a ranar asabar da ta gabata, kusa da inda ake fafatawa tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF, a yaƙin da suke yi tun a watan Afrilun shekarar 2023.
Shugaban WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya nemi a dakatar da kai wa cibiyoyin kiwon lafiya hari, duk da cewa bai ambaci sunan ɓangaren da ake zargi da kai wannan hari ba.
Sai dai ƙungiyoyin kare hakkin ɗan adam sun zargi wani jigin yaƙin sojojin Sudan marar matuƙi da kai wannan hari, da wata sanarwa da aka fitar a ƙarshen mako ta ce mutunen da suka mutu sun kai 9.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Kotu ta aike da mutumin da ake zargi da satar yaran Kano yana kaiwa Delta zuwa gidan gyaran hali
Babbar Kotun Jihar Kano a ranar Talata ta bayar da umarnin aikewa da Ogugua Christopher zuwa gidan gayarn hali bisa zarginsa da hannu a sata da kuma safarar yara daga jihar Kano zuwa kudancin Najeriya.
Ana dai zargin mutumin ne da mallakar wani gidan marayu a jihar Delta ba bisa ka’ida ba, sannan yana amfani da shi wajen ajiye yaran da ake zargin na sata ne a ciki.
Majalisa ta gayyaci CBN da bankunan kasuwanci kan yawan cire wa kwastomomi kuɗaɗe DAGA LARABA: Shin Ko Jam’iyyar PDP Ta Fara Gushewa Ne?Hukumar Hana Fatucin Mutane ta Kasa (NAPTIP) ce dai da gurfanar da Christopher tare da wasu abokar harkallarsa su biyu, Hauwa Abubakar da Nkechi Odlyne, wadanda su ba su je kotun ba a ranar.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Amina Adamu ce ta bayar da umarnin kullewar yayin fara sauraron shari’ar, bayan sauraron bukatar lauyan masu kara, Salisu Muhammad Tahir da na wanda ake karar, Gideon Uzo.
Daga nan ne kuma kotun ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Oktoba inda ake sa ran za a gurfanar da Christpher tare da sauran wadanda ake zargin.
An dai kama Chrispoher ne bayan wani samame da jami’an hukumar ta NAPTIP suka kai gidan nasa da ke jihar Delta sannan suka ceto yara takwas da ake zargin ya sace su daga Kano sannan ya kai su gidan marayun nasa da ke Asaba, babban birnin jihar ta Delta.