Sin Ta Yi Matukar Allah Wadai Da Hare-Haren Da Amurka Ta Kaiwa Iran
Published: 22nd, June 2025 GMT
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya ce Sin ta yi matukar Allah wadai da hare-haren da Amurka ta kai kasar Iran, tare da jefa bama-bamai kan cibiyoyin sarrafa nukiliyar kasar, dake karkashin kulawar hukumar lura da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ko IAEA a takaice.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana hakan ne a Lahadin nan, lokacin da yake tsokaci kan sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar, cewa Amurka ta kaddamar da hare-hare kan cibiyoyi uku na nukiliyar kasar Iran.
Daga nan sai jami’in ya ce Sin na kira ga sassa masu ruwa da tsaki a tashin hankalin dake wakana, musamman ma Isra’ila, da su gaggauta cimma matsayar dakatar da bude wuta, tare da tabbatar da tsaron rayukan fararen hula, da fara tattaunawa da shawarwari. Ya ce Sin a shirye take, ta yi aiki da sauran kasashe wajen aiwatar da matakan tabbatar da adalci, da aiki tukuru wajen dawo da yanayin zaman lafiya da daidaito a Gabas ta Tsakiya. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Jariri ya mutu a bayan uwarsa yayin tsere wa ’yan bindiga a Neja
Wani jariri ya rasu a bayan mahaifiyarsa a yayin da take guje wa harin ’yan bindiga a kauyen Allawa da ke Karamar Hukumar Shiroro a Jihar Neja.
Sarkin yankin Bassa, Bagudu Amos, ne ya bayyana hakan a lokacin taron tattaunawa da mata kan zaman lafiya da kare su daga cin zarafi, mai taken: “Ƙarfafa kariya daga cin zarafin jima’i da na jinsi a Jihar Neja.”
Kungiyar Tunani Initiative, tare da goyon bayan Dorothy Njemanze Foundation da Ford Foundation, ce ta shirya taron domin ƙarfafa mata wajen yaki da cin zarafi da ke ƙara ta’azzara a sakamakon rashin tsaro.
Bagudu Amos ya bayyana cewa mahaifiyar ta yi tafiya mai nisa a kafa da jaririn a bayanta domin tserewa daga harin ’yan bindiga, amma daga bisani ta gano cewa jaririn ya riga ya mutu a bayanta.
Yadda aka kashe jami’an tsaro 53 cikin mako biyu NAJERIYA A YAU: Yadda Wata Bakuwar Cuta Take Cin Naman Jikin Mutanen MalabuYa ce lamarin da ya faru a shekarar 2023, na ɗaya daga cikin dimbin abubuwan firgici da mata ’yan gudun hijira ke fuskanta a kullum, inda mafi yawansu ba su da isasshen tallafi ko ƙarfafa gwiwa wajen yaki da cin zarafin jinsi da ke biyo bayan matsalar tsaro.
Shugabar Tunani Initiative, Maryam Mairo Ibrahim, ta nuna damuwarta kan yadda ba a ba wa mata muhimmanci da ya dace wajen shiga cikin harkar sasanta rikice-rikice da zaman lafiya a Jihar Neja. Ta yi kira ga mata da su haɗa kai domin karya shingayen da ke hana su shiga harkokin warware rikice-rikice.
“A Jihar Neja, kamar yadda ake gani a wasu wuraren da ke fama da rashin tsaro, mata su ne mafiya fuskantar ƙuncin hare-haren ’yan bindiga. Idan an kai hari, mafi yawanci maza ake kashewa, sai a bar mata da nauyin sake gina iyali daga farko. Wannan rawar da mata ke takawa ba a ba shi muhimmancin da ya kamata. Wannan shi ne dalilin da ya sa taron ya mayar da hankali kan ƙara bayyana muhimmancin mata a harkar zaman lafiya da kuma yaki da cin zarafi,” in ji ta.
Daraktan Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam a Jihar Neja, Ambasada Nuhu Muhammad, ya jaddada muhimmancin samun karin mata a majalisar dokokin jiha da ma ta ƙasa domin samar da dokoki da manufofi da za su amfanar da su.
Mata da suka halarci taron sun yi kira da a tsaurara hukunci kan masu yi wa mata fyade, tare da kira da a haɗa ƙarfi da ƙarfafa juna wajen shawo kan yawaitar cin zarafi musamman a ƙauyuka.
Mahalarta sun kuma jaddada muhimmancin kafa ƙungiyar mata mai ƙarfi guda ɗaya domin tunkarar matsalar cin zarafin mata a Jihar Neja.