Leadership News Hausa:
2025-09-24@11:08:08 GMT

‘Yan Bindiga Sun Kashe Ɗan Kasuwa da Ɗan Banga A Kwara

Published: 25th, June 2025 GMT

‘Yan Bindiga Sun Kashe Ɗan Kasuwa da Ɗan Banga A Kwara

A cewar sanarwar, a ranar 22 ga watan Yuni, 2025, da misalin ƙarfe 10:40 na dare, wasu mutane huɗu ɗauke da bindigu sun kai farmaki gidan Alhaji Dauda, inda suka yi harbe-harbe sannan suka sace shi suka tafi da shi zuwa wani waje da ba a sani ba.

Nan da nan jami’an ‘yansanda, sojoji, ‘yan banga da masu farauta suka haɗa tawaga domin shiga daji don ceto mutumin.

Washegari da safe, ranar 23 ga watan Yuni, da misalin ƙarfe 7 na safe, tawagar ta haɗu da masu garkuwar a ƙauyen Korori.

Sai da aka yi musayar wuta, inda aka kashe ɗaya daga cikinsu, aka ƙwato bindiga ƙirar AK-47 mai harsashi 13.

Sauran kuwa suka tsere cikin daji, kuma ana ci gaba da nemansu.

Abin takaici, ɗan banga Haruna Tasusuno ya samu rauni sakamakon harbi, inda aka garzaya da shi asibiti kuma aka tabbatar da rasuwarsa daga baya.

An samu Alhaji Dauda kwance a daji cikin jini da raunukan sara da adda a jikinsa, kuma likita ya tabbatar da cewa ya rasu.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Ɗan banga Ɗan Kasuwa Kwara

এছাড়াও পড়ুন:

An kashe jami’an tsaro 53 a cikin mako biyu —Bincike

Aƙalla jami’an tsaro 53 aka kashe a sassa daban-daban na Nijeriya cikin makonni biyu da suka wuce, bisa ga ƙididdigar da muka tattaro daga rahotannin kafofin yaɗa labarai.

Jami’an da abin ya shafa sun haɗa da sojoji da ’yan sanda da jami’an Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula (NSCDC), jami’an shige da fice da na kwastam, da ma jami’an sa-kai da ke taimaka wa jami’an tsaro, ciki har da ’yan sa-kai na JTF da na ƙungiyoyin tsaro na al’umma da gwamnatocin jihohi suka kafa.

Yawancin waɗanda aka kashe, ’yan bindiga ne suka halaka su yayin da suke ƙoƙarin kare al’umma a lokacin hari, yayin da wasu kuma aka kashe su ne a wuraren binciken tsaro da sansanoninsu.

Wannan adadi ya taƙaita ne kan alkulman da muka tattara daga rahotannin kafofin yaɗa labarai, bai haɗa da wasu hare-haren da ba a bayyana su ba ba.

NAJERIYA A YAU: Yadda Wata Bakuwar Cuta Take Cin Naman Jikin Mutanen Malabu Mahara sun kashe ’yan sanda a shingen bincike a Kogi

Wani bincike da muka gudanar a watan Disambar bara ya nuna cewa, daga watan Janairu 2023 zuwa Oktoba 2024, aƙalla jami’an ’yan sanda 229 aka kashe a faɗin ƙasar nan.

Binciken ya bayyana cewa ’yan bindiga, ’yan ƙungiyar IPOB da ’yan Boko Haram da ’yan fashi da makami da kuma ’yan ƙungiyoyin asiri ne suka kashe jami’an tsaron.

Sabbin hare-haren sun faru ne a jihohin Benue da Kogi, inda aka kashe ’yan sanda bakwai da wasu jami’an tsaro a lokuta daban-daban a ranar Juma’a da kuma jiya Lahadi.

Baya ga waɗanda aka kashe, an kuma sace wasu jami’an tsaro a harin da aka kai a Binuwai.

A ’yan kwanakin nan, Hukumar Tsaro ta DSS ta gurfanar da mutane tara a gaban kotu bisa zargin hannu a kisan gilla da aka yi a jihohin Binuwai da Filato.

An kai su gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda kuma aka tuhumi wani da ake zargi da fataucin makamai bisa mallakar bindigogi ƙirar M16 guda bakwai ba bisa ƙa’ida ba.

Cikin waɗanda aka gurfanar har da Haruna Adamu da Muhammad Abdullahi, ’yan asalin Karamar Hukumar Awe a Jihar Nasarawa, da ake tuhuma da laifuka huɗu kan kashe-kashe a Abinsi da Yelewata a Ƙaramar Hukumar Guma ta Jihar Binuwai a ranar 13 ga watan Yuni.

Haka kuma an gurfanar da Terkende Ashuwa da Amos Alede, dukkansu daga Guma, kan zargin kai farmaki don ramuwar gayya da kuma lalata dukiya, wanda ya haddasa salwantar shanu 12 a garin Ukpam.

 

Daga:

Sagir Kano Saleh, Abdullateef Salau, Idowu Isamotu (Abuja), Hope Abah (Makurdi), Tijjani Labaran (Lokoja) & Abubakar Akote (Minna)

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Yanke Wa Sojojin Da Suka Sayar Wa ‘Yan Ta’adda Makamai Hukuncin Ɗaurin Rai-da-rai A Borno
  • ‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Filato
  • Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Da Ɓullar Cutar Mpox A Jihar
  • Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Ɓullar Cutar Mpox A Jihar
  • Mataimakin Shugaban BUK Ya Buƙaci ‘Yan Siyasa Da Su Yi Koyi Da Tallafin Karatu Na Barau
  • Cikin Mako 2, An Kashe Jami’an Tsaro 53 A Faɗin Nijeriya
  • An rufe sansanin NYSC da kasuwanni saboda rashin tsaro a Kwara
  • Karin ƙananan hukumomi 2 sun yi sulhu da ’yan bindiga a Katsina
  • An kashe jami’an tsaro 53 a cikin mako biyu —Bincike
  • Mahara sun kashe ’yan sanda a shingen bincike a Kogi