Trump ya soki Iran da Isra’ila kan saɓa wa yarjejeniyar tsagaita wuta
Published: 24th, June 2025 GMT
Shugaban Amurka Donald Trump ya soki Isra’ila da Iran, bayan zargin ƙasashen biyu da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da aka ƙulla.
Lamarin na zuwa ne bayan ɓullar rahoton kai wa juna hari daga dukkan ƙasashen biyu, duk da ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta ’yan sa’o’in da suka gabata.
Sarkin Musulmi ya ba da umarnin fara duban watan Muharram An tura ’yan China 6 kurkuku kan laifin ta’addanci a NijeriyaTrump ya ce ƙasashen sun daɗe suna faɗa da juna, kuma a wannan mataki ana iya cewa ba su ma san abin da suke yi ba.
Ya ce: “Ba abin da muke so ke nan ba, ina tabbatar muku cewa ina fushi da abin da suka aikata.”
Shugaba Trump ne mutum na farko da ya fara sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ilan da Iran, bayan shafe kwana 12 suna kai wa juna hare-hare.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Iran Isra ila yarjejeniyar tsagaita wuta
এছাড়াও পড়ুন:
Bayan Sulhu Da Ƴan Bindiga, An Saki Mutane 70 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina
Mutune 70 da aka yi garkuwa da su sun samu ƴanci a Jihar Katsina, bayan yarjejeniyar sulhu da aka ƙulla da fitaccen shugaban ƴan bindiga, Isiya Kwashen Garwa. A wani faifan bidiyo da ya bayyana, Garwa ya saki mutane 40 a ƙaramar hukumar Faskari, kwanaki biyu bayan ya fara sakin wasu 30, wanda hakan ya kai adadin zuwa 70 gaba ɗaya.
Rahotanni daga mazauna yankin sun ce sakin na baya-bayan nan ya biyo bayan tattaunawa tsakanin shugabannin al’umma da sansanin Garwa, a wani mataki da ake ganin zai rage tashin hankali da hare-hare a yankin. Duk da haka, Garwa ya nuna rashin jin daɗi kan abin da ya kira sumamen Sojoji a unguwar Ruwan Godiya a lokacin Sallar Juma’a, inda ya yi zargin cewa wasu Hausawa da Fulani sun samu raunuka. Ya gargaɗi cewa irin waɗannan hare-hare na iya rusa sulhun da aka ƙulla.
Abubuwan Da Ba A Faɗa Ba Game Sulhu Da Ƴan Bindiga A Katsina An Cafke Wani Magidanci Da Lafin Sojan Gona A KatsinaHukumomin jihar ba su fitar da wata sanarwa ba kan sumamen da ake zargin ba, sai dai majiyoyin tsaro sun ce an kai hare-haren ne kan maboyar ƴan ta’adda tare da nufin kare rayukan jama’a. Mutanen da aka sako, galibinsu manoma ne da aka sace daga ƙauyukan karkara a Faskari, suna cikin kulawar likitoci da kuma binciken tsaro kafin a mayar da su wurin iyalansu.
Gwamnatin jihar ta ce tattaunawa tana daga cikin dabarun tsaro da ake amfani da su, amma ta jaddada cewa dole ne ƴan bindiga su miƙa makamansu gaba ɗaya tare da fuskantar hukunci kan laifuffukan da suka aikata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp