Gwamnatin Gombe za ta biya ’yan fansho Naira biliyan 6.6 kuɗin ritaya
Published: 26th, June 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Gombe ta amince da fitar da Naira biliyan 6.563 kuɗin giratuti domin biyan haƙƙoƙin ’yan fansho da suka yi ritaya daga shekarar 2021 zuwa 2023.
Wannan sanarwar ta fito ne bayan taron Majalisar Zartarwa karo na 48 wanda Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya jagoranta.
Arsenal za ta ɗauki ɗan ƙwallon Brentford Christian Norgaard Za mu ci gaba da tattaunawa da Iran kan yarjejeniyar nukiliya — TrumpKwamishinan Kuɗi da Tattalin Arziki, Muhammad Gambo Magaji, ya bayyana cewa Naira biliyan 1.
Sannan kuma za a biya Naira biliyan 2.342 a watan Disamba ga waɗanda suka yi ritaya a shekarar 2023, kamar yadda kwamishinan ya bayyana.
Da wannan mataki dai gwamnatin za ta cike gibin bashin kuɗin giratuti da Gwamnatin Inuwa Yahaya ta gada, wanda ya kai sama da Naira biliyan 21 a shekarar 2019.
“Zuwa yanzu, an riga an biya sama da Naira biliyan 17, wanda ke nuna jajircewar gwamnatin wajen kula da jin daɗin ma’aikata.”
Da wannan biyan na baya-bayan nan, gwamnatin na gab da kammala biyan dukkan hakkokin giratuti daga shekarar 2014 zuwa 2023, wanda ke tabbatar da alkawarin ta ga wadanda suka yi ritaya tare da dawo da amana tsakanin gwamnati da al’umma.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Giratuti jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya da suka yi ritaya Naira biliyan
এছাড়াও পড়ুন:
Mata 400 sun amfana da kayan haihuwa a Gombe
Ƙaramar Hukumar Gombe, ta raba wa mata masu juna guda 400 kayan haihuwa kyauta, domin kare lafiyarsu da rage mace-mace a yankin.
An gudanar da rabon ne a Cibiyar Haihuwa ta Gombe a ranar Alhamis, inda shugaban Ƙaramar Hukumar, Barista Sani Ahmad Haruna, ya jagoranci rabon.
Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 4, 16 sun jikkata a Yobe Gwamnan Gombe ya bai wa maharba kyautar motoci da babura don bunƙasa tsaroShugaban ya ce shirin ya yi daidai da umarnin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, na bunƙasa kiwon lafiya a matakin farko, musamman ga mata masu juna biyu daga lokacin ɗaukar ciki har zuwa haihuwa.
Ya kuma bayyana cewa an fara gwajin jini kyauta ga mata masu juna biyu a dukkanin cibiyoyin haihuwa, domin gano matsalolin lafiya tun da wuri.
Wasu daga cikin matan da suka amfana sun gode wa gwamnati, inda suka bayyana cewa shirin zai rage musu kashe kuɗi tare da tabbatar da lafiyarsu da ta jariransu.
Wata mata mai suna Sa’adatu Garba, ta bayyana jin daɗinta game rabon kayan.
“Wannan kaya da aka ba mu tabbas za su taimaka, musamman duba da halin matsi da ake ciki,” in ji ta.
Ita kuwa Rabi Mustapha cewa ta yi: “Wannan babban tagomashi ne, muna godiya Allah Ya saka da alheri. Wannan shiri zai sauƙaƙa mana wajen rage kashe kuɗaɗe.”