A ƙalla mutane 15 ne suka mutu sakamakon sabon harin da ‘yan bindiga suka kai a daren Alhamis a ƙauyukan Manja a Mangu da Tangur a ƙaramar hukumar Bokkos, Jihar Filato. An kai harin ne a lokuta daban-daban, inda aka ce Manja aka fara kai hari kafin daga bisani aka farmaki Tangur da misalin ƙarfe 9 na dare.

Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun shigo ƙauyukan suna harbe-harbe ba tare da kakkautawa ba, sannan suka ɓalle gidaje suna kai hari. A cewar majiyar da ke cikin Mangu, mutane bakwai aka kashe a yankin, yayin da mutane takwas suka mutu a Bokkos.

EFCC Ta Kama Tsohon Kakakin Majalisar Filato Da Wasu ‘Yan Majalisa 14 Bisa Zargin Almundahana Sojoji Sun Damƙe Ɗan Fashi, Sun Kwato Makamai A Kaduna Da Filato

Shohotden Mathias Ibrahim, Daraktan Al’adu na ƙungiyar ci gaban Mwaghavul kuma Darakta a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Mangu, ya tabbatar da alƙaluman mace-macen a yankin Mangu. Ya bayyana cewa akwai matsanancin tashin hankali a cikin al’umma sakamakon harin.

Sai dai ƙoƙarin da wakilin Daily Trust ya yi na jin ta bakin wasu shugabanni da mazauna Bokkos bai yi nasara ba, yayin da kakakin ‘yansandan Jihar Filato, Alfred Alabo, bai amsa kiran waya da sakonni ba har zuwa lokacin haɗa rahoton nan da safe.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Army

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan bindiga sun kashe sojoji 3 a Kebbi 

’Yan bindiga sun kashe sojojin Nigeriya guda uku a wani kwanton ɓauna da suka yi masu a lokacin da suke ƙoƙarin hana yin garkuwa da wasu mutane a ƙauyukan ƙananan hukumomin Sakaba da Danko-Wasagu a Jihar Kebbi.

Sojojin da aka kashe an yi masu sutura a babban barikin sojoji da ke garin Zuru, hedikwatar ƙaramar hukumar Zuru.

Mai Martaba Sarkin Zuru Alhaji Sanusi Mika’ilu Sami, ya halarci janazar domin tausayawa da jinjina wa marigayin kan sadaukarwar da suka yi a wurin kare mutanen ƙasa.

Majiyar da ta shaida wa Aminiya ta ce sojojin sun kai ɗauki ne a lokacin da suka samu labarin ’yan ta’addan sun kai farmaki tare da ƙoƙarin yin garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa.

Rashin wutar lantarki ta kassara kasuwanci a Kaduna, Kano da Katsina ’Yan Najeriya miliyan 60 na fama da taɓin hankali — Likita

Sai dai ana jiran bayani daga rundunar soja ta kasa kan wadannan jami’ai nata da aka kashe a fagen daga a yakin jihar Kebbi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Rikicin kabilanci: Mutane 2 sun mutu, wasu 7 sun jikkata a Jigawa
  • Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27 Da Birnin Tarayya
  • Mutane A Fadin Duniya Sun Soki Ayyukan Neman ‘Yancin Kan Taiwan
  • Maryam Sanda na cikin waɗanda Tinubu ya yi wa afuwa
  • ’Yan sanda sun ceto mutum 10 daga hannun ’yan bindiga a Kaduna
  • Tinubu ya yi wa Maryam Sanda afuwa
  • ’Yan ta’adda sun kashe sojoji 4 a wani sabon hari a Borno
  • ‘Yansanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Wata Ba’amurkiya Da Ta Ziyarci Saurayinta A Jihar Delta
  • Mutane 2 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Kebbi
  • ’Yan bindiga sun kashe sojoji 3 a Kebbi