Bernado Silba Ya Zama Sabon Kyaftin Din Manchester City
Published: 22nd, June 2025 GMT
Kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya zabi dan wasan tsakiya Bernardo Silba a matsayin sabon kyaftin din kungiyar, jaridar Daily Mail ta rawaito Guardiola ya yanke hukuncin da kan sa inda ya ki ya nemi shawarar sauran yan wasan kungiyar, Silba ya maye gurbin Kebin De Bruyne bayan dan kasar Belgium din ya bar Etihad a karshen kwantiraginsa.
Guardiola ya kuma nada mataimakan kyaftin guda uku kafin fara gasar kakar wasa ta gaba da suka Ruben Dias, Rodri da Erling Haaland, Silba wanda kwantiraginsa zai kare a bazara mai zuwa, ka iya daura kambun kyaftin na Manchester City na kakar wasa daya kawai idan bai samu karin kwantiragi a kungiyar ba.
Jakadan Sin Dake Amurka Ya Yi Jawabi A Gun Liyafar Da Kwamitin Kasa Mai Lura Da Kasuwancin Amurka Da Sin Ya Shirya Atiku Da Wasu Sun Kafa Sabuwar Jam’iyya, Sun Nemi INEC Ta Musu RajistaDuk da cewa har yanzu bai rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya da City ba, Silba ya ki amincewa da tayin da dama na barin kungiyar a kasuwar musayar yan wasa na baya-bayan nan, kungiyoyin Saudiyya da dama na zawarcin dan wasan na Portugal, sai kuma tsohuwar kungiyarsa ta Benfica da itama ke fatan dawowarsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
’Yar shekara 17 daga Yobe ta lashe Gasar Turanci ta Duniya
Wata yarinya ’yar shekara 17, Nafisa Abdullah, daga Jihar Yobe, ta lashe Babbar Gasar Harshen Turanci ta Duniya ta ‘TeenEagle’ ta shekarar 2025 da aka gudanar a birnin Landan, fadar gwamnatin ƙasar Birtaniya.
Nafisa ta zama Gwarzuwar Shekarar 2025 ce baya da ta fafata ne da sama da mahalarta gasar 20,000 daga ƙasashe kusan 69 na duniya, inda ta zama ta ɗaya a Gasar ‘UK Global Finals’, sakamakon fintinkau da ta yi wa takwarorinta na ƙasashe daban-daban da ke jin harshen Ingilishi a duniya.
Wannan nasara ta lashe wannan babbar gasa da Nafisa ta samu ya haifar da alfahari a faɗin Najeriya, musamman a mahaifarta, Jihar Yobe. Nafisa ta wakilci Najeriya ne daga Kwalejin Tulip International College (NTIC), Jihar Yobe.
A wani jawabi da ya gabatar jim kaɗan da sanarwar lashe gasar, wani ɗan uwan Nafisa, Malam Hassan Salihu, ya yaba wa Gwamnatin Jihar Yobe da Makarantar NTIC bisa irin gudunmawar da suna bayar har ya kai ga samun nasarar ’yar uwarsa a wannan babbar gasa ta duniya. Ya ƙara da yaba wa shugabannin kwalejin bisa ga yadda suke gudanar da karatuttukansu da hakan ne ta kai ga nasarar.
Tinubu ya bai wa ’yan wasan ƙwallon kwandon mata kyautar Dala dubu 100 da gidaje Sanata Buba ya ƙaddamar da allurar rigakafin dabbobi kyauta“Tabbas wannan nasara da Nafisa ta samu da taimakon Allah (SWT) ne,” in ji shi, kuma nasarar wata babbar shaida ce ga abin da matasan Najeriya za su iya cimma idan aka ba su dama da goyon baya.
“Alal haƙiƙa wannan nasara da Nafisa ta samu ya zama abin farin ciki da alfahari ga duk al’ummar jiharmu ta Yobe da ma ƙasa baki daya,” in ji Malam Hassan.