’Yan bindiga sun kashe ɗan sanda, sun jikkata wasu 3 a Zariya
Published: 25th, June 2025 GMT
Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai wa motar ’yan sanda hari a Zariya, inda suka harbe ɗaya daga cikinsu har lahira, tare da raunata wasu uku.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:30 na daren ranar Talata, a unguwar Dalan Waje da ke kan hanyar Galadimawa, a Ƙaramar Hukumar Zariya da ke Jihar Kaduna.
A cewar wani mazaunin yankin da ya shaida faruwar lamarin, motar ‘yan sandan na bin wata mota ƙirar Golf kafin a ji ƙarar harbe-harbe.
Nan take mutane suka fara kwanciya a ƙasa domin tsira da rayukansu.
Wannan hari ya girgiza mazauna yankin, inda suka ce ko da yake yankin ya daɗe yana fama da hare-haren ’yan bindiga, amma an daɗe ba samu hari ba.
A harin, an kashe wani ɗan sanda mai suna Nasiru Musa.
Ɗan sandan mazaunin ƙofar Kibo ne a cikin birnin Zariya.
Sauran da suka jikkata sun haɗa da direban motar ’yan sandan, Auwalu Hassan Ɗan Jos, wani ɗan-sa-kai mai suna Awwal Hassan, Iliyasu Ya’u da Salisu Mohammed.
An garzaya da su zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, Zariya, domin samun kulawar likitoci.
Da Aminiya ta tuntuɓi kakakin ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansur Hassan, ya ce yana wajen wani taron sanin makamar aiki, don haka bai da cikakken bayani.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Yan Sanda Ɗan Sanda hari Zariya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Yusuf Ya Amince Da Korar Wasu Mataimaka Biyu Bisa Hannu Akan Belin Wani Dilan Miyagun Kwayoyi
Gwamnatin jihar Kano ta amince da korar wasu manyan mataimaka na musamman (SSAs) ba tare da bata lokaci ba, sakamakon zarge-zargen da wasu kwamitocin bincike suka yi na gudanar da bincike kan wasu laifuka.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Alhaji Umar Farouk Ibrahim ya fitar.
A wani gagarumin mataki da gwamnan ya dauka, ya amince da korar Abubakar Umar Sharada, babban mataimaki na musamman kan harkokin siyasa, bayan da kwamitin bincike na musamman ya tuhume shi a matsayin wanda ya shirya belin wani mai hatsarin gaske kuma dilan kwyaan maye, Sulaiman Aminu Danwawu, wanda ya tabbatar da laifin Abubakar Sharada a cikin takaddamar belin ta hanyar kwamitin da ya gabatar a gaban kwamitin.
A cewar wata wasika da ya fitar a ranar Juma’a, 8 ga watan Agusta 2025, ta hannun sakataren gwamnatin jihar (SSG), Sharada an umurce shi da ya mika dukkan kadarorin gwamnati da ke hannun sa ga babban sakatare, bincike, ranar Litinin, 11 ga Agusta 2025.
An kuma gargade shi da kada ya nuna kansa a matsayin jami’in gwamnati a wannan gwamnati mai ci.
Hakazalika, gwamnan ya sauke Tasiu Adamu Al’amin Roba, babban mataimaki na musamman, daga mukaminsa bayan kama shi da laifin sama da fadi da wasu buhunan hatsi a wani dakin ajiyar kaya da ke Sharada a shekarar 2024.
Tuni dai Roba ya gurfana a gaban kotu inda ake tuhumarsa da laifin sata da hada baki a kan zargin karkatar da kadarorin jama’a.
Haka kuma an umurci Tasiu Adamu Al’amin Roba da ya mika dukkan kadarorin gwamnati da ke hannun sa da suka hada da katin shaida a ranar Litinin ko kuma kafin ranar Litinin 11 ga watan Agusta 2025. Ya kuma yi gargadin kada ya bayyana kansa a matsayin ma’aikacin gwamnati a wannan gwamnati mai ci.
A wani labarin kuma, gwamnatin jihar ta wanke Hon. Musa Ado Tsamiya, mai ba shi shawara na musamman kan magudanun ruwa, wanda kwamitin bincike ya wanke shi daga dukkan zarge-zargen, inda ya tabbatar da cewa ba shi da laifi.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatin sa na tabbatar da adalci da kuma rashin hakuri da cin hanci da rashawa, yana mai gargadin dukkanin jami’an gwamnati da su kasance masu bin ka’ida mai inganci a ayyukansu da kuma rayuwarsu ta sirri.
A cikin wannan sanarwa, ana shawartar jama’a da kada su yi wata hulda da wadannan ‘yan siyasa biyu da aka kora a kan duk wani batu da ya shafi gwamnatin jihar Kano, duk wanda ya yi haka, ya yi ne a kan kansa.
Saki/Abdullahi jalaluddeen/Kano