Leadership News Hausa:
2025-06-20@11:05:00 GMT

Bikin Ranar Muhalli Ta Duniya: Akwai Babban Aiki A Gaban Nijeriya

Published: 20th, June 2025 GMT

Bikin Ranar Muhalli Ta Duniya: Akwai Babban Aiki A Gaban Nijeriya

Abbas ya kuma jaddada bukatar da dauki matakai, kan aukuwar sauyin yanayi, musamman duba da matsalar talauci da kuma ci gaba da fuskantar kalubalen rashin tsaro, da kasar nan, ke fuskanta.

Bugu da kari, Hukumar kula da ‘yan cirani ta duniya wato IOM ta sanar da cewa, gurbata muhalli da robobin da aka sarrafa zuke haifarwa, suna taka gudunmwa, wajen aukuwar dumamar yanayi da kuma gurbata muhalli.

A cewar Hukumar, matsalar na kuma lalata kasar noma da lalata hanyoyin ruwa, tare da kuma tilasta alumma, tashi daga matsugunan su, zuwa wasu gurare, domin su ci gaba da gudanar da rayuwarsu.

Hakazalika,  a cikin wasu rahotanni da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, sun bayyana cewa, a fadin duniya, ana yin amfani da Lidojin da suka kai, yawan miliyan 500 a duk shekara, wanda kusan tan miliyan 13, suke kwarara zuwa cikin Tekuna, a duk shekara.

Ana kuma yin amfani da Gangunan Mai miliyan 17, da aka sarrafa, aka kuma zuba a cikin Gangunan, inda kuma a fadin duniya, mutane ke sayen Kwalaben Man da suka kai miliyan daya.

An kiyasata cewa, a duk shekara, daobboin da ke rayuwa a cikin Tekuna  guda 100,000 ne, irin wadannan Robobin da aka zuba a cikin Tekunan, suke hallaka su.

Bugu da kari, wasu bincike da aka gudanar, sun nuna cewa, Ruwan sha da ake sarrafawa a sanya a cikin Robobin Shan Ruwa, sun kai kaso 90 a cikin dari, inda kuma Ruwan da ake samu daga Fanfuna, suka ke da kaso  83 a ckin dari, wadanda kuma suke dauke da sanadaran microplastic, da ke makalewa, a cikin Robobin, inda wannan sanadarin, ke shafar kiwon lafiyar bil Adama.

A Nijeriya za a iya cewa, kalubalen na muhalli sun kasance iri-iri, musamman duba da annobar ambaliyar ruwan sama da kasar ke fuskanta a duk lokacin damina da Fari da gurrbatar muhalli da kuma rashin samar da kyakyawan tsarin zubar da shara, musamman na bolar Robobin da aka gama amfani da su.

Misali, a ranar 28 na watan Mayun 2025, garin Mokwa, da ke a jihar Neja, an fuskanci, mummunar ambaliyar ruwan sama, inda jami’ai suka sanar da cewa, sama da mutane 200 da iftila’in ya aukwa, suka rasu tare da kuma bacewar mutane da yawansu ya kai sama da 1,000, wasu 121 suka samu raunuka, gidaje 2,000 suka lalace.

Irin wannan iftila’in na Mokwa, na daya daga cikin rin wadanda suka auku a shekarun baya a wasu sannan kasar.

Ana nan, muma mun goyi bayan furucin da Ministar Kula da Jindadi da Walwalar Mata Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim ta yi, na ciwar kalubalen na gurbatar muhlaii, na janyo tarwatsa alumomin kasar, daga matsugunan su, musamman duba da yadda iftila’in, yafi shafar mata da yara.

Batun da ake yi na samar da wadataccen abincin a kasar, zai kasance ne tamkar wani mafarki, matukar mahukutna kasar, ba su yi gaggawar daukar matakan da suka kamata, kan batun na gurbatar muhalli, a kasar ba.

Domin samar da tsarin rage zubar da bola, musamman ta Robobi a kasar Gwamnatin Tarayya ta gabatar da wani tsari na  NPPWM.

Sai dai, wannan tsarin ya hadu da cikas, musamman duba da cewa, wanzar da tsarin daga bangaren Gwamnatin, ba ta mayar da hankali akansa ba, inda sai dai kawai, daidaikun ‘yan kasar ne a kashin kansu suke ci gaba da tsaftace guraren da ake jibge bola, musamman a birane da wasu guraren.

Shugabar Babban Majalisi a Majalisar Dinkin Duniya Maria Fernanda Espinosa Garcés, ta bayar da shawarar cewa, batun na gurbar muhalli, abu ne, da ya wajaba a sake tunani akai.

A daukacin jihohi 36 na kasar, Legas da Ekiti ne kawai, suka dauki matakan da suka kamata, kan kare gurbatar muhalli, a jihohinsu.

Kazalika, a matakin Majalisa, Shugaban Kwamiti kan Yada Labarai da Kula da Hudda da Jama’a Hon. Akin Rotimi ya shelanta cewa, daga cikin kudurori 899 da Majalisar ta gabatar a cikin shekaru biyu, guda 27 ne kacal, Majalisar ta mayar da hankali kan na kula da muhalli.

Sai dai, an ruwaito cewa, wani Majalisar na kan kokrin samar da wasu tsare-tsare na yakar yawan amfani da Robobin barkatai a kasar, musamman a biranen kasar.

A ra’ayin wannan Jaridar, muna goyon bayan cewa, ba zai yuwa a bar Nijeriya a baya, wajen shiga cikin kokarin da ake yi, a fadin duniya, na yakar gurbata muhalli ba.

Ya zama wajbi, bikin na wannan shekarar, ya kasance mataki na farko, na yakar gurbata muhalli, ba wai kawai tatsuniya ba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Sojojin Nijeriya sun kashe gomman ’yan ta’adda a Tafkin Chadi

Rundunar sojin Nijeriya ta sanar dakashe gomman ’yan ta’adda na ISWAP da Boko Haram da suka yi ƙoƙarin kutsawa cikin sansanin sojin ruwan ƙasar a yankin Tafkin Chadi.

Hakan dai na kunshe cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na X ranar Laraba wadda ta ce ‘yan ta’addan sun yi ƙoƙarin kutsawa cikin sansanin sojojin ne da misalin ƙarfe 2 na dare, inda suka yi ƙoƙarin lalata sabbin motocin tafiya a fadama waɗanda gwamnatin Jihar Borno ta saya domin yashe hanyoyin ruwa.

Nijeriya za ta fara fitar ta tataccen mai zuwa Asia — Matatar Dangote HOTUNA: Yadda Tinubu ya ziyarci waɗanda suka jikkata a harin Benuwe

Sai dai jami’ai a sansanin sojin ruwan Nijeriya da ke Tafkin Chadin sun jajirce wajen hana su kutsawa, inda aka yi ta musayar wuta har tsawon sama da sa’o’i biyu kafin aka kai musu ɗauki daga Baga, lamarin da ya tilasta wa ‘yan ta’addan ja da baya ba tare da sun kai ga motocin tafiya cikin fadamar ba, in ji sanarwar.

Baya ga kashe gomman ‘yan ta’addan, sanarwar ta ce sojojin sun yi nasarar kwato ababe masu fashewa yayin da wasu daga cikin jam’ian tsaron suka ji rauni.

“Ɓangaren sojin sama [na rundunar] na bin sawun [‘yan ta’addan] a kan ruwa domin ƙara kassara su,” in ji sanarwar.

A makonnin baya bayan nan dai hare-haren ’yan Boko Haram suna ƙoƙarin dawowa arewa maso gabashin Nijeriya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisa Na Binciken Yadda Aka Kashe Naira Tiriliyan 1.12 Na Tallafin Manoma
  • 2027: ‘Sai bayan babban taron APC Tinubu zai bayyana wanda za su yi takara tare’
  • Xi Ya Tattauna Da Shugaban Rasha Ta Wayar Tarho
  • An Kashe Wasu ‘Yan Bindiga 12, An Kwato Makamai A Katsina
  • Dan Wasan Gaban Chelsea, Murdyk Ka Iya Shafe Shekaru 4 Ba Tare Da Ya Buga Wasa Ba
  • Sojojin Nijeriya sun kashe gomman ’yan ta’adda a Tafkin Chadi
  • Gwamnatin Tarayya Za Ta Kwaso ‘Yan Nijeriya Da Suka Maƙale A Isra’ila Da Iran
  • Xi Da Shugabannin Kasashe 5 Na Tsakiyar Asiya Sun Halarci Bikin Rattaba Hannu
  • Rikicin ƙabilanci ya yi ajalin mutum 20 a Chadi