Mun amince da tsagaita wuta da Iran —Isra’ila
Published: 24th, June 2025 GMT
Gwamnatin ƙasar Isra’ila ta ce ta amince da tsagaita wuta a yaƙin da aka kwana 12 ana gwabzawa tsakaninsu da Iran.
Isra’ila ta ce ta amince da shiga yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran ce bayan abin da ya kira cimma burinta na ƙaddamar da yaƙin a Iran tun a farko.
Ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa ta yi nasarar murƙushe duk wata barazanar da take fuskanta daga Iran na mallakar makamin nukiliya da makamai masu linzami.
Isra’ila ta ƙara da cewa ta kuma yi nasarar wargaza lissafin shugabancin sojin Iran da kuma lalata muhimman kadarorin gwamnatin ƙasar.
A karshe ta ce tanq godiya bisa abin da ya kira ƙoƙarin Shugaban Amurka Donald Trump na wargaza shirin nukiliyar Iran.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Iran Isra ila nukiliya
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun yi wa ’yan ta’adda ɓarin wuta a Borno
Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF), ta kai hare-hare ta sama a yankin Rann, wani gari da ke Jihar Borno, wanda ake zargin ya zama mafakar ’yan ta’adda.
Wannan aiki na cikin shirin Operation Haɗin Kai, kuma ya yi sanadin hallaka ’yan ta’adda da dama.
’Yan damfara 2 sun shiga hannun ’yan sanda a Yobe PDP ta gargaɗi ’ya’yanta kan goyon bayan Tinubu a zaɓen 2027Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa ’yan ta’addan sun fara guduws bayan yunƙurinsu na kai hari sansanin sojoji ya ci tura.
Da suka hangi jiragen yaƙi na sojojin sama, sai suka fara tserewa daga maɓoyarsu, amma an kashe da yawa daga cikinsu ta hanyar ɓarin wuta.
Wani mazaunin Rann ya ce da farko sun yi zaton cewa ’yan ta’addan ne za su kai musu hari saboda ƙarar da suka ji kamar ta bindiga.
Daga baya ne suka fahimci cewa sojoji ne ke gudanar da aiki.
Mai magana da yawun Rundunar Sojin Sama, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya tabbatar da harin a cikin wata sanarwa.
Ya ce sun samu bayanan sirri da suka tabbatar da inda ’yan ta’addan suke, kuma bayan sojojin ƙasa sun gano su suna guduwa, sai aka aike jiragen yaƙi da suka kai musu farmaki.
Harin ya daƙile barazanar ’yan ta’addan, kuma ya dawo da zaman lafiya a yankin.
Ejodame, ya ƙara da cewa wannan aiki ya nuna irin sadaukarwar da Rundunar Sojin Sama ke yi wajen kare dakarunta da kuma daƙile duk wata barazanar ’yan ta’adda.