Me Zai Faru Idan Iran Ta Datse Mashigar Hormuz Sanadiyar Hare-Haren Isra’ila?
Published: 22nd, June 2025 GMT
Hukumar kididdigar makamashi ta Amurka US Energy Information Administration (EIA) ta kiyasta cewa a farkon shekarar 2023 an yi dakon kusan ganga miliyan 20 na fetur a a kullum ta tekun.
Wannan ke nufin ana kasuwancin kusan dala biliyan 600 na makamashi duk shekara ta tekun.
Duk wani tsaiko a tekun zai iya jawo matsala a hada-hadar man fetur a duniya, wanda nan take za a iya gani ta hanyar tashin farashin man.
Sai dai masana suna gargadin cewa daukar wannan matakin zai iya zafafa rikicin na Isra’ila da Iran.
Wannan kuwa shi ne zai jawo wasu kasashen cikin rikicin, ciki har da Amurka, wadda take ta’allaka da man fetur daga kasashen Larabawa.
Yaya girman mashigar Hormuz?
Mashigar Hormuz na tsakanin Iran da Oman ne. Tekun na da fadin kilomita 50.
Taswirar tekun ta nuna bangarorin da suke da kyau a tsaya, da wuraren da ba a so a tsaya da kuma tudun mun tsira a tsakanin bangarorin biyu.
Idan tankokin mai za su wuce, sai su wuce ta kusa da tsibirin Greater da Lesser Tunb – inda ake takun-saka tsakanin Iran da kasashen Larabawa kan mallakinsa.
Masana sun ce yaki na cikin abubuwan da suke jawo tsaiko a hada-hada ta mashigar kamar yadda ya faru a yakin Iran da Iran a shekarar 1980 zuwa 1988.
Amfani da tekun domin kare kai?
Masana sun ce a wajen Iran, datse hada-hada a mashigar Hormuz na nufin amfani da wata dama domin kare kanta.
Kamar yadda kasashen duniya suka dade suna adawa da yunkurin Iran na samun nukiliya, manyan kasashen duniya sun sha nanata cewa ba za su bari Iran ta yi amfani da tekun ba wajen shake duniya game da samun makamashi.
Masana sun yi hasashen cewa Iran za ta iya datse mashigar na wani dan lokaci. Amma wasu na ganin Amurka da kawayenta ba za ta bari hakan ya dauki lokaci ba, inda suke hasashen Amurka za ta iya amfani da karfin soji wajen bude mashigar.
Ta yaya Iran za ta iya datse mashigar Hormuz?
A wani bincike da cibiyar bincike ta Congressional Research Serbice ta Amurka ta nuna, ta ce Iran za ta iya daukar matakin a hankali. Hanyoyin sun kunshi:
Sanar da hana sufurin jiragen ruwa ba tare da bayyana hukuncin saba dokar ba
Sanar da tantance jiragen dakon man ko kuma kwacewa
Yin barin wuta kan jiragen dakon
Kai farmaki kan wasu jiragen dakon
Binne wasu nakiyoyin ruwa a tekun
Kai farmaki kan wasu jiragen kasuwanci da na soji
A yakin Iran da Irak, Iran ta yi amfani da makamin Silkworm domin kai farmaki kan tankokin man fetur, sannan ta dasa nakiyoyi a cikin teku.
Daya daga cikin nakiyoyin ne ya fasa jirgin USS Samuel B Roberts, wanda ya sa Amurka ta mayar da martani.
Sai dai duk da haka Iran ba ta datse mashigar ba baki daya, amma ta kara harajin shige da fice, sannan taa lafta wasu ka’idoji da suka jawo cunkuson jirage wajen ficewa daga gabar tekun.
Ƙarfin sojin Iran
Kwana biyu kafin harin Isra’ila da ya kashe kwamandan dakarun juyin juya-halin Iran Manjo Janar Hossein Salami, kwamandan ya ziyarci sashen sojin ruwa da ke aiki a mashigar.
Ya bayyana yankin tekun a matsayin daya daga cikin muhimman yankunan kare kai da kasar ke da su.
Ya bayyana jirgin da zai iya tafiya tsawon kilomita 10 cikin minti uku a yankin.
Janar Salami ya ce za su yi amfani da manyan makaman masu cin dogon zango domin kare kasarsu. Ya kuma ce za su yi amfani da nakiyoyin ruwa.
Salami ya ce za su fadada ayyukan jirage maras matuka.
Me masana suke hasashe?
Masana suna hasashen daya daga cikin hanyoyin da Iran za ta bi domin datse dakon kusan jirage 3,000 da suke wucewa ta tekun a kusan duk wata ita ce dasa nakiyoyi da amfani da jirage masu cin dogon zango domin kai farmaki kan jiragen.
Sojojin Iran da dakarun juyin juya-hali na kasar za su iya kai farmaki kan jiragen dakon man kasashen waje.
Sai dai kuma Amurka da Isra’ila za su iya kai farmaki kan manyan jiragen ruwan soji idan Isra’ila suka yi amfani da su.
Yanzu haka kafar bibiya harkokin tekun kasar da ke amfani tauraron dan’adam sun nuna jiragen yakin Iran a yankin kudancin kasar.
Wadanne kasashe ne za su fi shiga cikin tasku?
Binciken da masana daga cibiyar Borteda suka yi ya nuna cewa Saudiyya tana fitar da danyen mai kusan ganga miliyan 6 a kullum ta Hormuz – sama da duk wata kasa a yankin.
China da India da Japan da Koriya ta Kudu na cikin manyan kasashen da sufurin danyen man fetur ta tekun.
EIA ta kiyasta cewa a 2022, kusan kashi 82 na danyen man fetur da ake dakonsa ta mashigar, kasashen Asia ake zuwa da su.
A ranar 16 ga watan Afrilun 2025, kwana uku kafin Isra’ila ta kai hari kan tsaron sararin samaniyar Iran, kamfanin dillancin labaran Iran IRNA ya ruwaito shugaban Afirka ta Kudu Yoon Suk-yeol ya ce kashi 60 na man fetur din kasar na biyowa ne ta mashigar Hormuz.
Haka kuma EIA ta ce Amurka na shigo da kusan ganga 700,000 na danyen mai ta mashigar a kullum – kimanin kashi 11 na man da take shigo da shi, kuma kashi uku da man da take amfani da shi a kasar.
kasashen turai baki daya ba sa shigo da fetur da ya haura sama da ganga miliyan 1 a kullum.
Don haka, kasashen Larabawa da Asia ne za su fi fuskantar kalubale idan aka datse mashigar, sama da Amurka da turai da suke da alakar siyasa da Isra’ila.
Sannan akwai kasashen Asia da dama da suke da alaka mai kyau da Iran.
Rawar da China za ta taka
China na cikin kasashen da suka fi amfani da man fetur da ake jigila ta Hormuz. Iran na sayar da mai a farashi mai rahusa, kasa da farashin kasuwannin duniya, wanda hakan ya sa kasar ke samun sauki kan takunkumin tattalin arziki da Amurka ta kakaba mata.
Saboda yadda take matukar amfani da man fetur, China ba za ta yi maraba da duk wani abu da zai jawo tashin farashin mai ba, ko kuma samun tsaiko a dakonsa. Wannan ya sa China za ta yi amfani da diflomasiyya wajen hana yiwuwar daukar wannan matakin.
Akwai wata hanya daban bayan tekun?
Saboda barazanar da ake yawan fuskanta ta datse mashigar a shekarun da suka gabata ne ya sa kasashen da suke dakon man fetur a yankin suka samar da wata hanyar daban.
Wani rahoton EIA ya ce Saudiyya ta fara amfani da bututun gabas maso yammaci mai nisan kilomita 1,200, wanda za a iya tura ganga miliyan 5 a kullum.
A shekarar 2019, Saudiyya ta gyara wasu bututun gas domin su yi daukar danyen man fetur.
Hadaddiyar Daular Larabawa ta hada gabar tekunta na tudu da gabar Fujairah da ke gabar Oma da bututun da zai iya daukar gangan mai miliyan 1.5.
A watan Yulin 2021, Iran ta kaddamar da bututun Greh-Jask, wanda zai iya jigilar mai zuwa gabar Oman. Yanzu haka bututun zai iya daukar ganga 350,000 a kullum.
Rahoton EIA ta kiyasta cewa wadannan hanyoyin za su iya jigilar ganga miliyan 3.5 a kullum – kusan kashi 15 na man da ake jigila ta tekun a kullum.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Iran Isra ila mashigar Hormuz kai farmaki kan datse mashigar ganga miliyan jiragen dakon ta mashigar
এছাড়াও পড়ুন:
Rasha da China sun fara wani gagarumin atisayen soji na hadin gwiwa a tekun Japan
Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta sanar a jiya Lahadi cewa, Sin da Rasha sun fara atisayen soja na hadin gwiwa mai taken “Tekun hadin gwiwa na shekarar 2025” a tekun Japan, a wani bangare na kokarin zurfafa hadin gwiwarsu ta fuskar “mutumin Amurka.”
Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta bayyana cewa, sojojin biyu za su gudanar da ayyukan ceto a cikin ruwa, da yaki na hadin gwiwa na yaki da jiragen ruwa, da na yaki da jiragen ruwa, da na jiragen ruwa a kusa da tashar jiragen ruwa na Vladivostok na Rasha.
Sanarwar ta ce, jiragen ruwa na kasar Sin 4 ne ke halartar atisayen tare da na Rasha, ciki har da makami mai linzami Shaoxing da Urumqi. Rasha da China za su gudanar da sintiri a tekun Pasifik bayan kammala atisayen na kwanaki uku.
Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta tabbatar a ranar Juma’a cewa, atisayen na shekarar 2025 na da nufin “zurfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare” a tsakanin kasashen biyu. Suna gaba da ziyarar da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin zai kai kasar Sin a karshen watan Agusta.
Putin zai halarci taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai da kuma bikin cika shekaru 80 da kawo karshen yakin duniya na biyu, ciki har da faretin soja, inda zai tattauna da shugaban kasar Sin Xi Jinping.
Kasashen biyu sun shafe shekaru suna gudanar da atisayen hadin gwiwa akai-akai, inda aka fara gudanar da atisayen “Tekun hadin gwiwa” tun daga shekarar 2012. An gudanar da atisayenSemin Joint-2024″ a gabar tekun kudancin kasar Sin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Araqchi Ya Bayyana Makomar Sinadarin Uranium Da Iran Ta Inganta A Lokacin Yaki August 3, 2025 Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Sun Bayyana Cewa: Masu Shirin Halaka Gaza Suna Son Mamaye Duniyar Musulmi Ne August 3, 2025 Iran Ta Jaddada Cewa: Karfin Makamai Masu Linzami Da Jiragen Sama Marasa Matuka Ciki Suna Nan Cikin Shiri August 3, 2025 Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Tana Kokarin Boye Barnarta A Zirin Gaza August 3, 2025 Tsohon Shugaban Amurka Joe Biden Ya Caccaki Trump Kan Rusa Kundin Tsarin Mulkin Kasar August 3, 2025 IRGC Tace Bata Amince Da Kasashen Biyu A Kan Kasar Falasdinu Ba August 3, 2025 Iran Da Japan Suna Iya Jagorantar Duniya Don Rabata Da Makamai Kare Dangi August 3, 2025 Kungiyar Hamas Ta Bayyana Cewa Ba za ta Ajiye Makamanta ba Sai Bayan samar Da Kasar falasdinu August 3, 2025 Kungiyar Hamas Ta Wallafa Hotunan bidiyo Na Fursinan HKI tsare A Gaza August 3, 2025 Sojojin HKI, Daga Jiya Zuwa Yau lahadi Kadai Sun Kashe Falasdinawa 62 August 3, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci