2027: Wajibi Ne A Saka Sakamakon Zaɓe A Na’ura – Farfesa Jega
Published: 23rd, June 2025 GMT
Batun sauya sheka da ke faruwa a cikin tsarin siyasar Nijeriya, Jega ya kira a hana sauya sheka ga wadanda aka zaba a bangaren zantarwa da kuma ‘yan majalisa.
Ya kuma yi kira ga jami’an INEC a matakin tarayya, da na jihohi su shirya gudanar da zaben cike gurbi da zarar an samu labari game da sauya sheka.
Ya ba da shawarar cewa ‘yan Nijeriya da ke zaune a kasashen waje su dunga kada kuri’a a zaben shugaban kasa, kuma ya yi kira a tsaurara dokoki kan kudaden kamfen ciki har samar da hukumar da za ta sa ido kan aiwatar da hukunci.
Jega ya yi nadama da cewa daya daga cikin manyan kalubalen da Nijeriya take fuskanta shi ne, yadda za a iya hana mulkin kama-karya, ” a cikin yanayin dimokuradiyya, tun daga shekarar 1999, lokacin da muka fara sauyi daga mulkin soja zuwa mulkin dimokuradiyya na farar hula.”
Ya ce, ‘Mun dauka ta hanyar dimokuradiyya kasarmu za ta samun ci gaba mai ma’ana da kyakkyawan shugabanci, amma sai dai lamarin ba haka yake ba.
“Abin takaici shi ne, bayan tsawon lokaci a cikin mulkin dimokuradiyya, maimakon karfafa dimokuradiyya, amma kuma an samu mulkin kama-karya a kasarmu kamar ba mulkin dimokuradiyya muke yi ba.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Mu daina zagin malaman addini idan muna son zaman lafiya — Uba Sani
Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani, ya gargadi ’yan siyasa da masu amfani da kafafen sada zumunta da su daina zagin malaman addini da a yanzu ya zama ruwan dare a ƙasar nan.
Gwamnan ya bayyana cewa irin wannan mummunar ɗabi’a ta cin zarafi malaman addini na iya lalata zamantakewa da tubalin zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin tattaunawarsa da malaman addini da na gargajiya a birnin Kaduna, inda ya jaddada muhimmancin rawar da shugabannin addini ke takawa wajen ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai.
Tinubu ya bai wa ’yan wasan ƙwallon kwandon mata kyautar Dala dubu 100 da gidaje Gwamnatin Kano ta karɓi rahoton binciken Kwamishinan da ya yi belin Danwawu“Ina nanata cewa, idan muka bari shugabannin addini suka zama abin zagi da cin mutunci ba gaira ba dalili, to ita kanta ƙasar nan za ta lalace balle wata jiha. Duk lokacin da abubuwa suka rikice, wurinsu muke komawa domin neman addu’o’i,” in ji Gwamnan.
Malam Uba Sani ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu ’yan siyasa ke haɗa kai da wasu da ya bayyana da “marasa sanin abin da ya dace” wajen ɓata suna da yi wa malamai ƙage a kafafen sada zumunta.
Ya buƙaci shugabanni da mabiyansu da su guji yin amfani da malaman addini wajen biyan buƙatun siyasa ko na ƙashin kai, yana mai jaddada cewa hakan yana barazana ga zaman lafiya da jituwa da ake morewa a Kaduna da ma ƙasar baki ɗaya.
Gwamnan ya kuma yaba da rawar da malaman addini suka taka tun daga lokacin da ya hau mulki har kawo yanzu, yana cewa sun kasance ginshiƙi wajen samar da zaman lafiya a jihar.
“Da ba don su ba, da babu damar da muke da ita yau ta cin moriyar zaman lafiya a Jihar Kaduna,” in ji shi.
Ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda ’yan siyasa ke watsi da malamai bayan samun nasarar zaɓe, sannan su sake waiwayarsu idan zaɓe ya gabato.
“Muna tunawa da su ne wata ɗaya ko biyu kafin zaɓe. Muna zuwa wajen su da maganganu na yaudara da daɗin baki dangane da addini, domin su mara mana baya.”
Uba Sani ya kuma buƙaci a samar da alaƙa ta dindindin da shugabannin addini, ba sai kawai lokacin da zaɓe ya kusanto ba.
“Malamai da shugabannin addini muhimman jiga-jigai ne a tsarin ƙasa, shi ya sa muke ganin lallai muna buƙatar su a koyaushe wajen shiriya, ba sai lokacin zaɓe ba,” in ji shi.
Ya ce tun farkon mulkinsa, ya samu shawarwari masu amfani daga shugabannin addini kan batutuwan zaman lafiya, haɗin kai da kwanciyar hankali a jihar.
A ƙarshe, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bai wa shugabannin al’umma muhimmanci a duk wani sha’ani da ya shafi tsaro, yana mai cewa zaman lafiya mai ɗorewa ba zai samu ba sai da amincewar jama’a da haɗin gwiwa.
“Mun bayyana cewa ba za mu tura jami’an tsaro zuwa kowace unguwa ba tare da tuntubar shugabannin yankin ba. Su za su ɗauki nauyi, su tsara, sannan gwamnati ta tallafa musu,” in ji gwamnan.