PDP ta mayar wa da na hannun damar Wike kujerarsa ta sakatarenta
Published: 25th, June 2025 GMT
Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta mayar da na hannun damar Ministan Abuja Nyesom Wike, wato Samuel Anyanwu kan kujerarsa ta Sakataren jam’iyyar na ƙasa.
Mai riƙon muƙamin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Iliya Damagum ne ya sanar da hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Laraba.
Yayin taron dai, shugaban na tare da Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.
Damagum ya ce yanke shawarar dawo da Anyanwu cikin kwamitin zartarwar jam’iyyar na ƙasa shawara ce mai wahalar gaske, amma ta sami goyon bayan mambobin kwamitin da dama.
Ya kuma sanar da cewa PDP ta soke taron kwamitinta na zartarwa da a baya aka yi yunkurin yi amma Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ba da shawarar dakatarwa.
Damagum ya kuma ce, “Za mu yi babban taron masu ruwa da tsaki a nan gaba, wanda daga nan ne za a tsara babban taron jam’iyyar.
“Anyanwu zai dawo kujerarsa ta Sakataren PDP na ƙasa, shi ya sa na ce shawara ce mai wahalar gaske. Kamar yadda INEC ta ce ba mu sanar da ita a kan lokaci ba, taron da za mu yi ranar 30 ga watan Yuni na masu ruwa da tsaki ne,” in ji shi.
A baya dai jam’iyyar ta dakatar da Anyanwu daga mukamin nasa sakamakon rikicin da ya dabaibaye ta wanda ta zargi Wiken da hannu a ciki.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Anyanwu
এছাড়াও পড়ুন:
Barin PDP Zuwa Wata Jam’iyyar Alamun Rashin Jarumta Ne – Gwamnan Bauchi
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP October 11, 2025
Siyasa Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu October 9, 2025
Labarai Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Da Aka Shigar Da Tinubu Kan Sanya Dokar Ta-Ɓaci A Ribas October 2, 2025