Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 19, Sun Ƙwato Makamai A Kano

Sojojin haɗin gwuiwa ta Operation MESA ƙarƙashin Birgediya ta 3 sun kashe ƴan bindiga 19 a ƙaramar hukumar Shanono ta jihar Kano, bayan wata musayar wuta mai tsanani da ta faru a yankunan Unguwan Tudu, Unguwan Tsamiya, da Goron Dutse da misalin ƙarfe 5:00 na yamma ranar Asabar. Wannan sumame ya biyo bayan sahihan bayanan leƙen asiri kan motsin wasu ƴan ta’adda da suka shiga yankin daga maƙwabtan dazuka.

A cewar sanarwar Kyaftin Babatunde Zubairu, Mataimakin Daraktan hulɗa da Jama’a na Birgediya ta 3, Sojojin tare da jami’an tsaro sun fatattaki ƴan ta’addan bayan musayar wuta, inda aka kashe ƴan bindiga 19, yayin da wasu suka gudu da raunin harbi. Ya ce an ƙwato babura da dama da kuma wayoyi guda biyu da aka samu a wajensu.

Mayar Da Martani Kan Barazanar Amurka Ga Nijeriya: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yaba Wa Kwankwaso  Kano Ta Amince Da Naira Biliyan 8.2 Don Ayyukan ilimi, Samar Da Ruwa, Da Makamashi

Sai dai, Sojoji biyu da jami’in sa-kai ɗaya sun rasa rayukansu yayin arta. Kyaftin Zubairu ya bayyana cewa sadaukarwar su hujja ce ta kishin ƙasa da jajircewar rundunar wajen kare ƴan Nijeriya da kawar da barazanar ta’addanci a yankin.

Kwamandan Brigade ta 3, Brigediya Janar Ahmed Tukur, ya yaba wa dakarun bisa jarumtarsu, yana mai tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da gudanar da aikace-aikacen tsabtace yankin domin hana ramuwar gayya da kare al’ummomin da ake yawan kai wa hare-hare. Ya kuma shawarci mazauna yankin da su ci gaba da lura da duk wani motsi na baƙuwar fuska da ba a saba gani ba tare da sanar da jami’an tsaro cikin lokaci.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Mayar Da Martani Kan Barazanar Amurka Ga Nijeriya: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yaba Wa Kwankwaso  November 3, 2025 Manyan Labarai Kano Ta Amince Da Naira Biliyan 8.2 Don Ayyukan ilimi, Samar Da Ruwa, Da Makamashi November 3, 2025 Manyan Labarai Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya November 2, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 19, Sun Ƙwato Makamai A Kano
  • Marasa Lafiya A Nasarawa Sun Koka Game Da Yajin Aikin Likitoci
  • Al’ummar Kauru Sun Koka Game Da Karuwar Hare-hare Da Ke Barazana Ga Gonaki Da Rayuka
  • Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik
  • Gidauniyar IRM Da KADCHMA, Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna
  • Pezeshkian: Bunkasa Masana’antar Makamashin Nukiliyar Iran Don Inganta Rayuwar Al’ummar Iran Ne
  • Araqchi: Da Hadin Bakin Amurka, Gwamnatin Isra’ila ta kaddamar Da Hari Kan Kasar Iran
  • Tsokaci Dangane Da Juyin Mulki A Nahiyar Afirka
  • An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya
  • Waye Zai Lashe Ƙyautar Gwarzon Ɗan Wasan Afrika Na 2025?