2027: Manyan ’Yan adawa na neman rajistar sabuwar jam’iyya
Published: 20th, June 2025 GMT
Jagororin jam’iyyun adawa na Najeriya a ƙarƙashin ƙungiyar hadaƙa ta Nigeria National Coalition Group (NNCG) na neman yin rajistar All Democratic Alliance (ADA) domin ta zama sabuwar jam’iyyar da za su yi amfani da ita don tunkarar Jam’iyyar APC a zaɓen 2027.
NNCG ta riga ta miƙa takardar neman rajistar jam’iyya ga Hukumar Zaɓe mai zaman kanta INEC a hukumance don babban zaɓe na gaba.                
      
				
Takardar wadda suka aika zuwa ga shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu a ranar 19 ga watan Yuni, wanda shugaban ADA na ƙasa Cif Akin Ricketts da sakataren riƙo Abdullahi Musa Elayo ne suka sanya mata hannu, sannan INEC ta karɓa tare a ranar Juma’a 20 ga Yunin.
A takardar an rubuta cewa, “muna neman INEC ta amince da buƙatarmu ta yi wa ƙungiyarmu ta All Democratic Alliance (ADA) ta zama jam’iyyar siyasa.”
Ta ƙara da cewa, taken jam’iyyar dai shi ne ‘Adalci ga kowa’ sannan masara ce tambarinta.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Alhaji Atiku Abubakar
এছাড়াও পড়ুন:
Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Yabawa Gwamna Namadi Bisa Ayyukan Hanyoyi A Fadin Jihar
Daga Usman Mohammed Zaria
Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu, Injiniya (Dr.) Muhammad Uba, ya yaba wa Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, bisa amincewa da sabbin ayyukan gina hanyoyi a fadin jihar, ciki har da na Birnin Kudu.
Ya ce wannan mataki na cikin ajandar gwamnati 12, musamman wajen inganta ci gaban ababen more rayuwa.
A cewarsa, Birnin Kudu za ta amfana da gina hanyoyi masu tsawon kilomita 113, wanda ya hada da hanyoyin kauyuka da wadanda ke hada al’umma da sauran sassan jihar.
Dr. Uba ya bayyana aikin a matsayin babban ci gaba wajen saukaka zirga-zirga, inganta harkokin tattalin arziki da samun sauki ga muhimman ayyuka ga jama’a.
Ya bayyana tabbacin cewa za a dade ana cin moriyar aikin hanyoyin, tare da hanzar ayyukan ci gaba da bunkasar karamar hukumar.
Shugaban ya yi addu’ar dorewar zaman lafiya da cigaba a Birnin Kudu tare da yin alkawarin ci gaba da hada kai da gwamnatin jiha domin tabbatar da cewa jama’a suna amfana da fa’idodin dimokuraɗiyya.