Hajjin Bana: Jihohi 11 Sun Kashe Naira Biliyan 6.2 Kan Mahajjata
Published: 21st, June 2025 GMT
Haka zalika, Gwamnatin Jihar Kebbi ba ta bayar da tallafi ga mahajjantanta 3,800 daga jihar ba. Amma a kasar Saudiyya, Gwamnan Nasir Idris ya amince da bayar da Riyal 200 ga kowane alhaji daga jihar.
Gwamnatin Jihar Lagos ba ta tallafi ga mahajjatanta a wannan shekara ba, yayin da kowane daga cikin masu aikin hajji 1,315 daga jihar ya biya kimanin naira miliyan 9.                
      
				
Amma kuma, Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ba kowane daga cikin mahajjatan kyauta Riyal 180, wanda ya kai naira 98,454,050 gaba dayansu.
Gwamnatin Jihar Jigawa, wacce ma ba ta bayar da tallafi ga mahajjatanta ba a wannan shekarar, amma ta ba su kyautar Riyal 100 (kimanin naira 43,000) ga kowanne daga cikin mahajjatanta 930.
Dukkanin alhazai Jihar Sakkwato 3,200 sun karbi Riyal 1,000 (wanda ya kai kimanin naira 450,000) a matsayin kyautar sallah daga Gwamna Ahmed Aliyu.
Gwamnan ya sanar da hakan a ranar Asabar yayin ziyararsa ga tawagar alhazan jihar a Mina da ke kasar Saudiyya, inda ya taya su murnar kammala aikin hajj cikin nasara.
Mataimakin gwamnan Jihar Borno, Umar Usman Kadafur, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta biya kudin hadiyya ga kowane alhazi daga jihar. Adadin alhazan sun kai 2,174, da suka yi aikin hajji a wannan shekara daga jihar.
Wani masani kan harkokin al’umma, Farfesa Yahaya Tanko, a cikin wata hirar, ya bayyana cewa kashe kudin da gwamnonin suka yi kan aikin hajji ba matsala ba ce, amma sun manta da asalin abin da al’ummarsu suka fi bukata.
Ya ce ya kamata gwamnonin su fi mai da hankali kan magance matsalar tsaro da inganta jin dadin ‘yan kasa.
Da yake jawabi kan lamarin, babban limanin Al-Habibiyah Islamic Society (AIS), Sheikh Fuad Adeyemi, ya ce ba laifi ba ne ga gwamnatin tarayya da na jihohi su tallafa wa masu alhazai, amma ya kamata a yi amfani da kudaden wajen abubuwan da mutane suka fi bukata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano
Majiyar ta kara da cewa, bayan yunkurinsu bai yi nasara ba a Tsanyawa, maharan sun sake wani sabon shiri, inda suka kai hari a kauyen Yar Tsamiya da ke gundumar Faruruwa, karamar hukumar Shanono, da misalin karfe 1:30 na dare, inda suka kashe mutane uku suka, tare da sace wasu uku.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA