Sarkin Musulmi ya ba da umarnin fara duban watan Muharram
Published: 24th, June 2025 GMT
Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ya da umarnin fara duban watan Muharram na sabuwar shekarar musulunci ta 1447 daga gobe Laraba, 29 ga watan Zulhijjan 1446, wanda ya yi daidai da 25 ga watan Yulin 2025.
Hakan na ƙunshe cikin wata takarda da Wazirin Sakkwato kuma shugaban kwamitin bai wa majalisar Sarkin Musulmi shawara kan harkokin addinin musulunci, Farfesa Sambo Wali Junaid ya raba wa manema labarai.
Sarkin Musulmi ya ce duk wanda ya samu ganin jinjirin watan ya sanar wa hakimi ko uban ƙasa mafi kusa da shi don sanar da majalisar sarkin musulmi.
A ƙarshe sanarwar ta ce Sarkin ya roƙi Allah Ya kawo wa Nijeriya zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa.
Watan Muharram dai shi na wata na farko kalandar Musulunci wanda ake maraba da zuwansa yayin da ake bankwana da shekarar musulunci ta 1446 Bayan Hijira.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Muharram Sarkin Musulmi Sarkin Musulmi
এছাড়াও পড়ুন:
ASUU Ta Janye Yajin Aiki Bayan Gwamnatin Tarayya Ta Biya Albashin Watan Yuni
Wannan matakin ya biyo bayan shawarar Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na ASUU wanda ya amince da tsarin “Ba Albashi, Ba Aiki” saboda yawan jinkirin biyan albashi da suke fuskanta.
ASUU ta ɗora laifin hakan kan Ofishin Akanta-Janar na Tarayya.
Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Chris Piwuna, ya bayyana a ranar Litinin cewa gwamnatin na nuna halin ko-in-kula kan batun.
Ya ce duk da yawan ganawa da jami’an gwamnati, malamai na fuskantar jinkirin albashi ba tare da wani dalili ba.
“Muna so mu yi aiki, amma ba za mu iya ba saboda ba su ba mu damar yin haka ba. Wannan aiki ne da aka yi da gangan. Matsalar ba daga wajen tsarin biyan albashi ba ne, matsalar tana wajen mutanen da ke da alhakin sakin kuɗin ne,” in ji Piwuna.
Ya ƙara da cewa sauyi tsarin biyan albashi daga IPPIS zuwa GIFMIS ya ƙara jefa malamai cikin wahala.
ASUU ta ce duk wata Jami’a da ba a biya malamanta albashin Yuni kafin 7 ga Yuli ba, to, ya kamata su fara yajin aiki nan take.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp