Guguwar ruwan sama ta yi ɓarna a Kwalejin Kimiyya da Fasaha a Kogi
Published: 19th, June 2025 GMT
An samu rahoton cewa guguwar ruwan sama ta yi ɓarna a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya (Federal Polytechnic), Idah a Jihar Kogi, inda ta ɓarnata kadarori da gine-gine da dama.
Rahoton na cewa, wata mummunar guguwar ruwan sama da ta biyo bayan ruwan sama da aka kwashe tsawon sa’o’i ana yi a ranar Laraba ce ta haddasa barnar, inda ta lalata rufin gine-gine da tagar gine-gine da dama a makarantar.
Ana cikin haka, an ba da rahoton cewa ɗakunan karatu da ɗakunan gwaje-gwaje da ɗakunan kwanan ɗalibai da ke cikin harabar kwalejin guguwar ruwan saman ta haddasa mummunar ɓarna.
Shugaban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya Idah, Dokta Yakubu Usman, ya ce, “Wannan abu ne mai ban tsoro ga Kwalejin a irin wannan lokaci, muna baƙin ciki da irin ɓarnar da guguwar ta yi.
“Har yanzu muna kan tantance irin ɓarnar da guguwar ta yi domin sanin asarar kuɗi wajen gyarawa da kuma dawo da wuraren da suka lalace yadda suke.
“Ya zuwa yanzu matakin ɓarnar ya kai ga Gwamnatin Tarayya ce kawai za ta iya shiga tsakani a iya fitar da cibiyar daga wannan yanayin cikin sauri”.
Dakta Usman ya ƙara da cewa, cibiyar za ta yi duk mai yiwuwa wajen bayar da tallafin da ya dace ga wuraren da abin ya shafa domin ɗalibai su ci gaba da harkokin karatu ba tare da ɓata lokaci ba
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: guguwar ruwan sama
এছাড়াও পড়ুন:
Shirin kashe N712bn kan gyaran filin jirgin Legas ya tayar da ƙura
Amincewar Gwamnatin Tarayya da kashe Naira biliyan 712 biliyan don gyaran Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas ya haifar da ce-ce-ku-ce a faɗin Najeriya.
Wannan gagarumin kashe kuɗi, da Majalisar Zartarwa ta Kasa ta amince da shi a ranar Alhamis da ta gabata, ya sanya masana harkar jiragen sama, ’yan adawa, da kuma jama’ar ƙasa yin tambayoyi game da buƙatarsa, tsadarsa, da kuma inda za a samo kuɗin.
Masu suka suna nuna yadda kuɗin ya yi yawa, har ya ninka kuɗin da aka ware wa Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama a kasafin kuɗin 2025 har sau goma. Hasali ma aikin ba ya cikin kasafin 2025.
Wannan ya sa wasu ke kiran aikin a matsayin “almubazaranci,” musamman ganin halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki.
Wani babban abin da ke haifar da surutan shi ne tsarin samo kuɗin. Gwamnati ta sanar da cewa za a samu kuɗin ne daga Asusun Ayyukan Raya Kasa na Renewed Hope Infrastructure Development Fund.
Amma jam’iyyun adawa, ciki har da ADC, sun ce Majalisar Dokoki ta Ƙasa ba ta amince da wannan kashe kuɗi ba, don haka suka kira shi “kashe kuɗi ba tare da kasafi ba.”
Yunkurinmu na jin ta bakin kakakin Majalisar Dattawa da ta Wakilai ya ci tura, wanda hakan ya ƙara ɓoye sirrin aikin.
Gyaran tashar jirgin ta Legas, wanda aka ba kamfanin gine-gine na CCECC kwangilar, zai haɗa da kwance ginin gaba ɗaya sannan a sake gina sabbin na’urorin zamani da tsarin lantarki da ruwa.
Wasu ayyukan sun haɗa da kwangilar Naira biliyan 44.13 na sabbin fitilun titin jirgin, Naira biliyan 24.27 na faɗaɗa wuraren ajiye jiragen sama, da kuma shingen tsaro . mai ɗauke da na’urorin zamani na Naira biliyan 49.9.
Jimillar kuɗin ta kuma haɗa da irin waɗannan gyare-gyaren a filayen jiragen sama na Kano da Fatakwal.
Wannan ba shi ne yunkurin farko na gyara filin jirgin na Legas ba. Tsohuwar gwamnatin Marigayi Muhammadu Buhari ta buɗe wani sabon tashar jirgin a shekarar 2022, wanda aka gina da kuɗin rancen dala miliyan 500 daga ƙasar China.
Amma wannan tashar ta fuskanci matsaloli masu yawa, inda kamfanonin jiragen sama da yawa suka ƙi amfani da ita saboda ƙarancin wurin ajiye manyan jirage.
Sabuwar tashar ta kasance ba a amfani da ita na tsawon fiye da shekara guda, inda yawancin kamfanonin jiragen sama na duniya ke ci gaba da amfani da tsohuwar tashar da yanzu aka shirya wa gagarumin gyara.
Yayin da gwamnati ke ci gaba da shirin ta, cece-kucen ya ƙara ta’azzara.
Tare da rashin samun cikakken bayani daga hukumomin Majalisar Dokoki da kuma tarihin ayyukan filayen jiragen sama da suka tsaya, jama’a na ci gaba da shakkar gaskiyar kuɗin da za a kashe da kuma nasarar da za a samu a wannan sabon aiki.