EFCC ya kama manyan jami’an NNPC kan badaƙalar Dala 7.2bn
Published: 24th, June 2025 GMT
Hukumar EFCC mai yaki da masu karya tattalin arziki ta tsare wasu tsofafin manyan jami’an Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) kan zargin badakalar kudade da yawansu ya kai Dala biliyan 7.2.
Jami’an EFCC sun tsare tsohon Babban Jami’in Kudi na NNPCL, Umar Ajiya Isah da kuma tsohon Manajan-Daraktan Matatar Mai ta Warri, Jimoh Olasunkanmi, kan zargin almundahanar.
Wani babban jami’in EFCC da ya nemi a boye sunansa ya ce hukumar ta tsare tsoffin manyan jami’an na NNPC ne kan zargin wadaka da kudaden gyaran matatun mai da ke Kaduna da Warri da kuma Fatakwal.
Wakilinmu ya yi kokarin samun karin haske daga kakakin EFCC, Dele Oyewale, amma jami’in bai amsa duk kiraye-kirayen da aka yi masa da kuma rubutattun sakon da aka tura masa domin samun bayani a hukumance.
Umar Ajiya ya kasance mai kula da harkokin kula da kudaden gyaran matatun guda uku da kuma da kuma manyan jami’an da ke aiki.
Iran ta kama ’yan leƙen asirin Isra’ila 6 Iyalan Kanawa da aka kashe a Uromi sun zargin gwamnati da yin watsi da suWani jami’in EFCC ya bayyana cewa hukumar tana kuma bincikar was jami’an NNPC da ke kula da wasu muhimman ayyuka kan zargin su da karkatar da kudade da kuma karbar na-goro daga ’yan kwangila.
A cewarsa, wadanda binciken ya shafa sun hada da Manajan-Daraktan Matatar Warri, Tunde Bakare; tsohon Manajan-Daraktan Matatar Fatakwal, Ahmed Adamu Diko da wani tsohon Manajan-Daraktan matatar, Ibrahim Monday Onoja.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan kwangila Matatar mai Manajan Daraktan manyan jami an
এছাড়াও পড়ুন:
Trump ya zargi Isra’ila da Iran da saɓa yarjejeniyar tsagaita wuta
Shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump ya zargi Iran da Isra’ila da saɓa yarjejeniyar tsagaita wuta.
Da yake jawabi kafin tafiyar Babban Taron Ƙungiyar NATO, da zai gudana a birnin Hague, Trump, ya bayyana takaicinsa bisa yadda kasashen biyu game da saɓa yarjejeniyar, sa’o’i kaɗan bayan sun amince da ita.
Tun da farko sai da ya buƙaci Isra’ila ta janye shirinta na kai wa Iran hari.
A safiyar Litinin bayan sanarwar Trump cewa ɓangarorin sun amince su tsagaita wuta ne, Ministan Tsaron Isra’ila ya yi barazanar kai wa Iran hari mai tsanani bayan zargin ta da harbo wa ƙasarsa rokoki.
Iran ta musanta zargin tare da cewa Isra’ila za ta yaba wa aya zaƙi idan kuskura ta kawo mata hari.
Daga bisani Trump ya ce wa Isra’ilar, “Kada ki kai harin bom a Iran, yin kika babban saɓawa ne. Ki umarci matuƙa jiragenkinki su koma gida.”
Buƙatar tasa bayan fara tsagaita wuta da Iran ta yi, na da alaƙa da sabon tayar da jijiyoyin wuts tsakanin Iran da Isra’ila.