A yau Jumma’a, ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta bayyana cewa, a cikin watanni biyar na farkon shekarar 2025, an kafa sabbin kamfanoni na kasashen waje guda 24,018 a babban yankin kasar Sin, wanda ya nuna an samu karuwarsu da kashi 10.4 bisa dari a mizanin shekara-shekara.

Daga watan Janairu zuwa Mayu, ainihin jimillar jarin waje na kai-tsaye, watau FDI da aka yi amfani da shi a masana’antun fasahohin kasar Sin ta kai yuan biliyan 109.

04, inda jarin na FDI ya karu da kashi 146 cikin 100 a fannin hada-hadar kasuwanci ta shafin intanet, da kashi 74.9 cikin 100 a fannin kera kayayayakin jiragen sama, da kashi 59.2 bisa 100 a fannin samar da sinadaran harhada magunguna, da kuma karin kashi 20 cikin 100 a fannin kera na’urori da kayayyakin aikin likitanci. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB

Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta sanar da samun nasarar cafke Ifeanyi Eze Okorienta, wanda aka fi sani da “Gentle de Yahoo”, ɗaya daga cikin manyan kwamandojin ƙungiyar IPOB, a wani samame da ta kai a yankin kudu maso gabashin ƙasar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito wata majiya daga hedikwatar rundunar sojin tana cewa an cafke Gentle de Yahoo ne yayin farmakin da sojojin suka kai a ranar Lahadi kan sansanonin ’yan ƙungiyar a cikin wani dajin da ke ƙaramar hukumar Okigwe a Jihar Imo.

An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas

Majiyar ta ce a yayin cafke jagoran na IPOB, an kuma ƙwato makamai da dama daga hannunsa, ciki har da bindigogi kirar Turai, harsasai, kakin sojoji da na ’yan sanda.

“Cafke wannan kwamanda babban ci gaba ne wajen murƙushe ayyukan ta’addanci da ƙungiyar IPOB ke aikatawa, musamman a yankunan da suke hana zaman lafiya,” in ji majiyar.

Kungiyar IPOB, wacce ke fafutukar ballewa daga Najeriya don kafa ƙasar Biyafara, ta kasance a gaba-gaba wajen aikata hare-hare da ta da tarzoma a jihohin kudu maso gabas, musamman ta hannun sashen rundunar da suka kafa da kansu mai suna Eastern Security Network (ESN).

Ana dai zargin cewa Eze yana ɗaya daga cikin jagororin da ke tsara harin kwantan bauna, da hana zirga-zirga a wasu sassan yankin, wanda hakan ya jefa al’umma cikin fargaba da zaman ɗar-ɗar.

Wannan nasara na zuwa ne bayan makonni kaɗan da wata kotu a ƙasar Finland ta yanke wa Simon Ekpa, wani babban jigo a ƙungiyar IPOB, hukuncin ɗaurin shekaru shida a gidan yari kan laifukan da suka shafi ta’addanci da tayar da zaune tsaye.

Masu sharhi na ganin cewa cafke Gentle de Yahoo wata alama ce da ke nuna cewa ana shirin ragargaza ƙungiyar IPOB gaba ɗaya, duk da cewar har yanzu akwai sauran rina a kaba, musamman ganin cewa wasu sassan yankin na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato
  • Yakin Haraji Da Cinikayya Ba Zai Gurgunta Fifikon Da Sin Ke Da Shi A Fannin Raya Masana’antun Sarrafa Hajoji Da Kasar Ta Gina A Tsawon Lokaci Ba
  • An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
  • Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire
  • Kungiyar Human Rights Watch; Isra’ila Ta Kashe ‘Yan Jarida Fiye Da 30 A Kasar Yemen Ne Da Gangan  
  • ’Yan ‘Mafiya’ na ƙoƙarin kashe matatar man fetur da na gina —Ɗangote
  • Sabunta Cinikin Ba Da Hidima, Masu Zuba Jari Na Waje Suna Ganin “Damar Da Kowa Ke Bukata A Kowane Lungu Na Sin”
  • Bayanin Bayan Taron Doha Ya Yi Kira Da A Kafa Runduwar Hadin Gwiwa Ta Kare Kai
  • Burkina Faso: Masu Ikirarin Jihadi Sun Kashe Fararen Hula 50 A Cikin Watanni Hudu
  • An kama mabaraci da kuɗaɗen ƙasar waje a Ilorin