Za a dawo da dukkan Alhazai gida ranar 28 ga Yuni – NAHCON
Published: 19th, June 2025 GMT
Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta tabbatar da aniyarta na dawo da dukkan Alhazan Najeriya da ke Saudiyya zuwa ranar 28 ga watan Yunin, 2025.
Rahotanni daga Hukumar NAHCON da ke birnin Makkah na cewa, alhazan Najeriya 6,528 ne suka dawo Najeriya, yayin da Kamfanin Max Air ya kammala jigilar Alhazai jirgi na 16 a ranar Talata.
Wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktan yaɗa labarai Fatima Sanda Usara ta fitar ta ce NAHCON tare da hukumar jin daɗin alhazai ta jiha, da kuma masu jigilar jiragen sama na shekarar 2025 suna yin duk abin da za su iya don ƙara saurin jigilar.
“Hukumar ta shirya dawo da dukkan alhazan nan da ranar 28 ga watan Yuni 2025 kuma ta ci gaba da zage damtse don jigilar.
“A cikin wannan lokaci, dukkan ƙasashen suna ƙoƙarin dawo da alhazansu a lokaci guda, kuma hakan ya haifar da tsananin buƙatar filayen jiragen sama.
“Waɗannan gurbi na Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama (GACA) da ke Saudi Arabiya ne ke kula da su, kuma a halin yanzu, ba a ware wa Nijeriya gurabe masu yawa kamar yadda ake buƙata domin tafiyar da alhazai masu yawa cikin gaggawa.
“Saboda haka, manyan masu ruwa da tsaki a harkar sufurin jiragen sama guda uku sun tsara dabarun ƙara yawan wuraren da za a samu a ƙasar.
“Ana fatan tattaunawa mai ƙarfi da mahukuntan Saudiyya za ta taimaka wajen ƙara yawan filayen jiragen.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON Saudiyya
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Matakin hana malaman da ba su da rajista hawa mumbari a Neja yana ci gaba da yamutsa hazo a ciki da wajen jihar.
Yayin da wasu suke ganin wannan mataki bai dace ba, wasu kuwa gani suke faduwa ta zo daidai da zama, wato matakin ya zo a daidai lokacin da ake bukata.
NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau UkuShirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kan tanadin Dokar Kasa game da wannan batu.
Domin sauke shirin, latsa nan