Iran Da Isra’ila Sun Amince Su Tsagaita Wuta – Trump
Published: 24th, June 2025 GMT
Sai dai babu wani tabbaci daga gwamnatin Iran ko Isra’ila kan cewa sun yarda su dakatar da yaƙin.
Trump ya kira rikicin da ake ciki da suna “yaƙin kwana 12,” yana mai cewa wannan rikici da za a iya yin shekaru ana fafatawa da shi bai bazu ba, kuma ba zai bazu ba.
Mene ne ke faruwa yanzu?
Bayan da Trump ya sanar da cewa an tsagaita wuta, Isra’ila ta ce an kashe mutane uku sakamakon hare-haren da Iran ta kai.
Amma ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce babu wata yarjejeniya ta tsagaita wuta.
Sai dai ya ce Iran za ta daina kai hari idan Isra’ila ma ta dakatar da nata.
Rikicin ya tsananta ne bayan Iran ta kai hari sansanin sojin Amurka da ke Qatar, wanda ya sa Trump ya nemi a dakatar da faɗan.
Me Iran da Isra’ila suka ce?
Gidan talabijin na Iran (IRINN) ya ce an tsagaita wuta ne bayan da Iran ta samu nasara a harin da ta kai.
Sun ce Trump ne ya roƙi a daina faɗam.
Ministan harkokin wajen Iran ya ce Iran ta daina kai hari tun ƙarfe 4 na dare, idan har Isra’ila za ta daina nata.
Har yanzu Isra’ila ba ta fitar da wata sanarwa ba kan tsagaita wutar, sai dai bayan sanarwar Trump, Isra’ila ta sake kai hari Iran.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Jihohin Makwabta, Ya Kara Ta’azzarar Rashin Tsaro A Neja – Bago
Ya kuma lura da cewa, tattaunawa da ‘yan bindiga a wasu jihohin suka yi ya kara ta’azzara satar shanu, inda ya ce, Sam hakan, ba za a amince da shi ba.
Dangane da ta’azzarar rashin tsaro, Gwamna Bago ya ce, za a nemi taimako daga shugaba Bola Tinubu da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp