Arsenal za ta ɗauki ɗan ƙwallon Brentford Christian Norgaard
Published: 26th, June 2025 GMT
Arsenal na fatan sayen ɗan ƙwallon Brentford, Christian Norgaard, da zai maye gurbin Thomas Partey.
Wasu majiya na cewa farashin da Arsenal za ta ɗauki ɗan wasan na tawagar Denmark mai shekara 31, zai kai £10m da karin £5m idan ya taka rawar gani da karin tsarabe-tsarabe.
Za mu ci gaba da tattaunawa da Iran kan yarjejeniyar nukiliya — Trump ’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 2, sun kama wasu a KadunaArsenal ta daɗe tana zawarcin Norgaard, wanda tanzu take fatan zai maye gurbin ɗan kasar Ghana, mai shekara 32, wanda bai amince da ƙunshin yarjejeniyar da Arsenal ta gabatar masa, domin ya ci gaba da taka mata leda.
Kwantaragin Partey za ta kare a mako mai zuwa, idan kuma ba a kai ga cimma wata yarjejeniya ba, zai bar Gunners.
Norgaard, wanda yake da sauran yarjejeniya da Brentford zuwa 2027 ya koma ƙungiyar a 2019 daga nan ya zama kashin baya a karkashin Thomas Frank, wanda ya koma horar da Tottenham.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Arsenal Christian Norgaard Thomas Partey
এছাড়াও পড়ুন:
Yanayin Sashen Samar Da Gidaje Na Sin Ya Kara Inganta Tsakanin 2021 Zuwa 2025
Ministan gidaje da raya birane da karkara na kasar Sin Ni Hong, ya ce yanayin sashen samar da gidaje na Sin ya kara inganta tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025, yayin aiwatar da manufar raya kasa karo na 14, inda jimillar adadin sayar da sabbin gidaje na kasuwa ya kai fadin sakwaya mita biliyan biyar.
Ni Hong, ya bayyana hakan ne a yau Asabar, yayin wani taron manema labarai. A cewarsa, sama da Sinawa miliyan 110 sun amfana daga babban tsarin gyaran tsofaffin gidaje cikin shekarun biyar. Kazalika, tsofaffin gidaje dake unguwanni sama da 240,000 a sassan biranen Sin, sun mori shirin gyaran fuska cikin wa’adin. Don haka gaba daya, yanayin ingancin muhallin biranen Sin ya kara inganta yadda ya kamata. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA