Majalisar Dattawa Na Nazarin Shawarwari 31, Da Ƴancin Ƙananan Hukumomi
Published: 24th, June 2025 GMT
2. Gyaran zaɓe da shari’o’in zaɓe
3. Ƙirƙirar sabbin jihohi
4. Samar da Ƴansandan jihohi
5. Haɗa kai don gudanar da mulki
Daga cikin muhimman shawarwari, akwai na kafa hukumar zaɓen ƙananan hukumomi (NALGEC), ƙara kujeru ga mata a majalisu, da ba wa ‘yan Nijeriya dake ƙasashen waje damar yin zaɓe.
Hakanan, akwai shawarwarin sauya wasu abubuwa daga jerin abubuwan da majalisar tarayya ke da ikon yi zuwa na majalisun jihohi, da kuma ƙirƙirar Majalisar Sarakuna ta ƙasa.
Kwamitin ya yi kira ga duk ‘yan ƙasa da su halarci tarurrukan sauraron ra’ayin jama’a da za a gudanar a:
– Lagos (Kudu maso Yamma)
– Enugu (Kudu maso Gabas)
– Ikot Ekpene (Kudu maso Kudu)
– Jos (Arewa Tsakiya)
– Maiduguri (Arewa maso Gabas)
– Kano (Arewa maso Yamma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Bai kamata ake bai wa ɓarayi muƙamin minista ba — Sarki Sanusi II
Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya ce bai dace a riƙa bai wa mutanen da suka wawure dukiyar ƙasa manyan muƙaman gwamnati kamar ministoci ba.
A cikin shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, Sanusi II, ya bayyana damuwarsa game da yadda ’yan Najeriya ke son dukiya fiye da gaskiya da tarbiyya.
Yadda sabbin takunkuman Trump za su shafi tattalin arziƙin duniya Ma’aikatan gwamnati na amfani da kudaden sata wajen gina rukunin gidaje – EFCCYa ce al’umma na girmama masu kuɗi, ko da kuwa an san kuɗin haram ne.
“Ƙasar da ke bai wa mutanen da aka san sun wawure dukiyar ƙasa muƙamin minista, za ta ci gaba da tafiya a doro mara kyau,” in ji Sanusi.
“Ba ma jin kunya idan wani ɗan siyasa ya tara dukiya ta hanyar da ba ta dace ba, sai ma mu yi masa tafi.”
Sanusi ya ce mutane da dama yanzu na shiga siyasa ne don su tara kuɗi, ba don su yi wa jama’a aiki ba.
Ya ƙara da cewa irin waɗannan shugabanni suna auna darajarsu ne da adadin gidajen da suke da su, jiragen sama masu zaman kansu, ko kuɗaɗe a asusun banki.
Ya ce ba su damu da irin kyakkyawan tasirin da suka yi wa al’umma ba.
Ya kuma ce rashin tarbiyya da gaskiya a tsakanin shugabanni na ƙara raunana tsarin gwamnati gaba ɗaya.
A cewarsa, wasu ba su damu da abin da mutane za su ce game da su ba muddin sun mallaki dukiya.
Yayin da yake tunawa da tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Murtala Muhammed, Sanusi ya ce Najeriya na buƙatar dawo da kyawawan ɗabi’u irin na shugabannin da suka gabace mu.
“Muna buƙatar daidaita ɗabi’unmu gaba ɗaya,” in ji shi.
“Ba wai shugaban ƙasa ko gwamnoni kaɗai ba ne za su canja ƙasa, kowa na da rawar da zai taka.”
Ya ƙara da cewa ’yan siyasa sun lalata tsarin aikin gwamnati, kuma Najeriya na buƙatar gina tsari mai ƙarfi da zai bai wa ma’aikatan gwamnati damar ƙin amincewa idan suka nemi su karya doka.
Sanusi, ya jaddada cewa kamata ya yi al’ummar Najeriya ta bai wa ɗabi’u kamar gaskiya, aiki tuƙuru, da tausayawa fifiko sama da tara dukiya.