Sin Ta Sha Alwashin Rarraba Fasahohinta Na Ainihi Da Dabarunta Na Kirkire-Kirkire Tare Da Sauran Sassan Kasa Da Kasa
Published: 26th, June 2025 GMT
Firaministan kasar Sin Li Qiang ya ce, kasarsa a shirye take ta rarraba fasahohinta na ainihi, da dabarunta na kirkire-kirkire tare da sauran sassan kasa da kasa. Li Qiang ya bayyana hakan ne cikin jawabinsa na bude taron shekara-shekara, na sabbin jagorori karo na 16, wato dandalin tattalin arzikin duniya na lokacin zafi na Davos a takaice, wanda aka bude yau Laraba a birnin Tianjin na kasar Sin.
Li ya kara da cewa, Sin na da karfin gwiwa, da ikon wanzar da ci gaban tattalin arzikinta, tana kuma kara kaimin zama kasa mai babban matsayin samun kudin shiga, yayin da ake kara daga matsayin sayayya bisa kyakkyawan yanayi a kasar, wadda ita ce ta biyu a girman kasuwar sayayya a duniya.
Firaministan na Sin ya kuma yi kira ga kasashen duniya, da su aiwatar da managartan matakan bunkasa hadin gwiwa a fannonin raya tattalin arziki da cinikayya. Ya ce hakan na nufin rungumar matakai na hakika, don kare tsarin cinikayya cikin ’yanci, da cudanyar mabanbantan sassa, da goya baya ga daidaitaccen tsarin raya tattalin arzikin duniya. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Sama Sun Yi Lugudan Wuta, Sun Kashe Ƴan Ta’adda A Borno
Rundunar Sojin Sama ta ƙasa (NAF) ta daƙile harin da ’yan ta’adda suka shirya kai wa sansanin Sojoji a Rann, jihar Borno, tare da kashe da dama daga cikinsu yayin da suke tserewa.
Mai magana da yawun NAF, Ehimen Ejodame, ya bayyana cewa dakarun saman ƙarƙashin Operation Haɗin Kai (OPHK) sun hana harin ne da safiyar 8 ga Agusta, 2025, ta hanyar samun bayanan leƙen asiri da kai farmaki daga sama.
Tashin Gurneti Ya Hallaka Yara Uku A Borno Sojoji Sun Kama Mai Yi Wa Boko Haram Safarar Man Fetur A BornoAn gano tarin ƴan ta’adda da ke gudu bayan samun bayanan sirri, sannan aka fatattake su da makamai na musamman, inda aka hallaka da dama daga cikinsu.
Ejodame ya ce wannan matakin gaggawar da aka ɗauka ya dawo da zaman lafiya a yankin, yana kuma nuna jajircewar NAF wajen kare Sojoji da shawo kan barazanar ƴan ta’adda cikin hanzari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp