NAJERIYA A YAU: Yadda ‘Yan Najeriya Za Su Kula Da Lafiyar Jikin Su
Published: 26th, June 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Kula da lafiya na nufin yin abubuwa da ke kare mutum daga kamuwa da cututtuka da kuma tabbatar da cewa jiki na aiki yadda ya kamata.
Wannan ya haɗa da cin abinci mai gina jiki, motsa jiki akai-akai, da dai sauran su.
Sai dai a wannan zamani ‘yan Najeriya ba kasafai suke kula da lafiyar jikin su ba, a mafi yawan lokuta ma sai ciwo ya kwantar da mutum sannan yake tunawa da likita.
Ko wadanne matakai ya kamata ‘yan Najeriya su ringa dauka wajen kare kan su da ma lafiyar jikin su? NAJERIYA A YAU: Dabarun Samun Kuɗaɗe Ta Hanyar Amfani Da Wayar Hannu DAGA LARABA: Ko Najeriya Na Da Kudin Renon Sabbin Jihohi?
Shirin Najeriya A YAU na wannan lokaci zai yi nazari ne kan yadda ‘yan Najeriya zasu dinga kula da lafiyar jikin su.
Domin sauke shirn, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: kula da lafiya lafiyar jiki
এছাড়াও পড়ুন:
Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi ta bar babban gibi a Najeriya – Tinubu
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana kaduwa da rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci kuma jagoran Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Fitaccen malamin ya rasu a Bauchi ranar Alhamis yana da shekaru 101.
Abubuwa 20 da ya kamata ku sani game da Sheikh Dahiru Bauchi Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban AmurkaA cikin wata sanarwa da Kakakin shugaban, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya bayyana Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin jagoran da ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa, wa’azi da jagorantar al’ummar Musulmi.
Tinubu ya ce rasuwar malamin ba wai asara ce ga iyalansa da almajiransa kawai ba, har ma ga ƙasa baki ɗaya.
“Sheikh Dahiru Bauchi malami ne, uba ne kuma murya ce ta daidaito da hikima. A matsayinsa na mai wa’azi kuma babban mai fassarar Alƙur’ani mai tsarki, ya kasance mai kira ga zaman lafiya da tsoron Allah. Rasuwarsa ta bar babban gibi,” in ji Shugaban Ƙasa.
Ya tuna da albarka da ya samu daga marigayin a lokacin shirye-shiryen zaɓen 2023.
Shugaban Ƙasa ya miƙa ta’aziyya ga almajiran malamin a faɗin Najeriya da wajen ƙasar, yana mai kira da su dawwamar da sunansa ta hanyar bin koyarwarsa ta zaman lafiya, tsoron Allah da kyautatawa ɗan adam.