Aminiya:
2025-11-08@14:22:35 GMT

HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar ’yan ɗaurin auren da aka kashe a Filato

Published: 22nd, June 2025 GMT

An yi jana’izar ’yan ɗaurin auren da aka kashe a garin Mangu, da ke Ƙaramar Hukumar Mangu ta Jihar Filato.

Waɗanda aka kashe sun haɗa da maza, mata da yara.

Dole a ɗauki mataki kan waɗanda suka kashe ’yan ɗaurin aure a Filato — Uba Sani Mahaifin Rahama Sadau ya rasu

Dukkaninsu mazauna unguwar Basawa-Anguwan Rimi ne da ke Ƙaramar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna.

Sun tashi ne daga Zariya zuwa Ƙaramar Hukumar Qua’an Pan da ke Jihar Filato domin halartar ɗaurin aure, amma aka kai musu hari a hanya.

An yi jana’izarsu tare da birne su da yammacin ranar Asabar a maƙabartar Hayi, ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro.

Malamai a Mangu sun ce iyalan mamatan sun amince a birne su a Filato domin kaucewa shiga tashin hankali a garinsu.

Kafin yi musu jana’iza, malamai sun roƙi Musulmai su ɗauki lamarin a matsayin ƙaddara daga Allah, su kuma guji ɗaukar doka a hannunsu.

Sheikh Suleiman Haruna, ɗaya daga cikin malamai a yankin da ya jagoranci jana’izar, ya buƙaci jama’a da su zauna lafiya tare da yin haƙuri da juna.

Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya yi Allah-wadai da harin, inda ya umarci jami’an tsaro da su kamo masu hannu a lamarin.

Ga hotunan yadda jana’izar ta wakana:

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ɗaurin Aure hari Zariya

এছাড়াও পড়ুন:

An kashe babban limami a Kwara saboda zargin maita

Wasu fusatattun matasa a ƙauyen Sokupkpan da ke karamar hukumar Edu a jihar Kwara, sun kashe Babban Limamin yankin, Mallam Abdullahi Audu, bisa zargin shi da alhaki kan mutuwar wani matashi, Ibrahim Gana ta hanyar maita.

Shaidu sun ce lamarin da ya faru a ranar Laraba ya jefa al’ummar yankin cikin rudani da firgici.

Gwamnatin Tarayya ta fara shirin sayar da matatun manta ga ’yan kasuwa Za a gudanar da wasannin ƙwallon yashi a Abuja

An ce wannan farmakin ya samo asali ne daga zargin cewa limamin ya yi amfani da maita wajen cutar da mamacin.

A cewar majiyoyi, kafin rasuwarsa, Gana ya dade yana fama da wata cuta da ba a bayyana ba, kuma ya sha faɗa cewa Babban Limamin yana damunsa a mafarki.

An ce ya sha gaya wa abokai da danginsa cewa limamin ne ke haddasa tabarbarewar lafiyarsa ta hanyar sihiri.

“Yayin da lafiyarsa ke ƙara tabarbarewa, mutane suka fara yarda da zargin nasa. Da ya mutu, wasu matasa suka yanke shawarar cewa limamin ne ke da laifi,” in ji wata majiya daga yankin.

A ranar Laraba, rikici ya ƙara ƙamari yayin da ’yan uwan mamacin – Mohammed Shaba, Mamudu Gana, da Ndakpotun Issa, suka tara wasu matasa don tunkarar limamin.

Duk da ƙoƙarin wasu dattawa na kwantar da hankali, gungun matasan sun kai wa limamin hari, inda suka lakada masa duka har ya ce ga garinku nan.

“Sun afka wa limamin suna zarginsa da kashe Gana ta hanyar sihiri. Sun ƙi sauraron duk wanda ya yi ƙoƙarin dakatar da su,” in ji wata majiyar.

’Yan sanda daga ofishinsu na Tsaragi sun isa yankin bayan faruwar lamarin, inda suka kama wasu da ake zargi da jagorancin harin.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Kwara, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis, tana mai bayyana shi a matsayin “kisan gilla mai ban tsoro.”

Ta ce binciken farko ya nuna cewa bayan mutuwar Gana mai shekaru 25 a ranar 4 ga watan Nuwamba, ’yan uwansa Mohammed Shaba da Mahmud Gana sun zargi Babban Limamin da haddasa mutuwarsa, kuma suka tara wasu don kashe shi.

A cewarta, “An kama mutane huɗu, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin kama sauran da suka shiga lamarin.”

Ta ce Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Adekimi Ojo, ya yi alla-wadai da lamarin, yana mai gargaɗin jama’a da su guji ɗaukar doka a hannunsu.

Tuni da aka yi jana’izar limamin bisa koyarwar addinin Musulunci.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna
  • Ɗan shekara 2 ya rasu bayan faɗawa rijiya a Kano
  • Gwamnatin tarayya ki amince damu a matakin ƙasa – Bijilanti
  • Yadda Duniya Ta Fara Wayewa Tun Daga Zamanin Annabi Nuhu (AS) Har Manzon Allah (SAW) Ya Zo Ya Cika Komai (2)
  • Kwalara ta kashe mutum 10 a Ƙaramar Hukumar Adamawa
  • An kashe babban limami a Kwara saboda zargin maita
  • Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i
  • An amince da hukuncin yi wa malamai ɗaurin shekara 14 kan lalata da ɗalibai
  • Yara biyu sun mutu bayan faɗawa rijiya a Kano
  • Zulum ya bai wa hukumomin tsaro kyautar motoci 63 don inganta tsaro a Borno