Aminiya:
2025-09-17@23:28:58 GMT

Muna shawartar Trump kada ya shiga yaƙin Iran da Isra’ila — Birtaniya

Published: 20th, June 2025 GMT

Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya buƙaci Donald Trump kada ya ɗauki matakin soji kan Iran, yana mai kiran da a biyo wa lamarin ta hanyar lalama.

Mista Starmer ya ce akwai “mummunan hatsarin bazuwar” yaƙin, inda ya yi kira ga duka ɓangarorin sun rungumi sulhu.

Ba zai yiwu mu bar Khamenei a raye ba — Isra’ila Hisbah ta lalata katan 243 na barasa da wasu kayan maye a Yobe

Ya ƙara da cewa a baya an samu “jerin tattauna masu yawa da Amurka, kuma ina ganin wannan ita ce hanyar warware matsalar.

Kalaman nasa na zuwa ne yayin da sakataren harkokin wajensa, David Lammy ke shirin ganawa da takwaransa na Amurka, Marco Rubio kan yadda za a taƙaita bazuwar yaƙin.

Da maraicen yau Alhamis ne kuma Mista Lammy da Mista Rubio suka gana domin tattauna halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya.

Su ma shugabannin China da na Rasha sun yi Alla-wadai da hare-haren Isra’ila kan Iran tare da kiran a tsagaita wuta.

Shugaba Xi Jinping da Vladimir Putin sun tattauna ta waya inda suka nuna goyon-bayan amfani da hanyoyin diflomasiya wajen shawo kan rikicin.

Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Aragchi zai tattauna da takwarorinsa na Faransa da Jamus da Birtaniya a Geneva a gobe Juma’a.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Birtaniya Iran Keir Starmer

এছাড়াও পড়ুন:

Sin Da Amurka Sun Yi Tattaunawar Keke-da-keke Kan Batutuwan Cinikayya Da Manhajar TikTok

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Bude Dandalin Tattauna Batutuwan Tsaro Na Xiangshan Karo Na 12 A Beijing 
  • Za A Kada Kuri’ar Raba Gardama Akan Sabon Tsarin Mulki A Kasar Guinea
  • An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe
  • Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima
  • Ma’aikatar Shari’ar Iran Ta Sanar Da Rataye Dan Leken Asirin Hukumar Mossad Ta Isra’ila
  • Iran Ta Bukaci Musulmi Su Goyi Bayan Yunkurin Kasa da Ka Na Kauracewa Isra’ila
  • Sin Da Amurka Sun Yi Tattaunawar Keke-da-keke Kan Batutuwan Cinikayya Da Manhajar TikTok
  • Iran Ta Bukaci IAEA Tayi Tir Da Harin Da Isra’ila Ta Kai A Tashoshin Nukiyarta.
  • Ministan Tsaron Kasar venezuela Ya Gargadi Amurka Dangane Da Kokarin Juyin Mulki A Kasar
  • Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Dakatar Da Shuka Kiyayya Da Tashin-Tashina A Tekun Kudancin Sin