Cristiano Ronaldo Na Shirin Tsawaita Kwantiraginsa A Kungiyar Al-Nassr
Published: 26th, June 2025 GMT
Dan wasan mai shekaru 40 ya zura kwallaye 93 sannan ya taimaka wajen zura 19 a wasanni 105 da ya buga a dukkanin wasannin da ya buga a kungiyar ta Saudiyya, amma har yanzu bai samu nasarar lashe kofi a gasar ba, a kakar wasan da aka kammala kwanan nan, Al Nassr ta kare a matsayi na uku a teburin, inda ta rasa gurbi a gasar cin kofin zakarun yankin Asia na shekara mai zuwa kuma a maimakon haka za ta buga gasar AFC Champions League 2.
Bugu da kari, Al Nassr a halin yanzu ba ta da koci tun bayan da ta raba gari da babban kocinta Stefano Pioli a ranar Laraba, wanda ya zama koci na uku da ya bar kungiyar tun bayan zuwan Ronaldo daga Manchester United.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Da Ɗumi-ɗumi: Gwamnan Ribas, Fubara Ya Ziyarci Tinubu A Fadar Gwamnati A Abuja
A halin yanzu, shugaba Bola Tinubu yana ganawa da gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara a fadar shugaban kasa dake Abuja a yammacin yau Litinin. Ganawar na zuwa ne kwanaki kadan bayan Fubara ya koma ofis a ranar 19 ga watan Satumba bayan da Shugaba Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da aka kafa a jihar Ribas tun farko. Tinubu ya bayyana matakin ne domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali bayan shafe watanni ana rikicin siyasa da ke barazana ga harkokin mulki da tsaro a jihar mai arzikin man fetur. Cikakken bayanai na nan tafe…
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp